Jami'an Tsaro Sun Samu Gagarumar Nasara kan 'Yan Bindiga a Katsina
- Jami'an tsaro sun yi nasarar daƙile wani mugun nufi da ƴan bindiga suka shirya a kan wasu ƙauyuka biyu na jihar Katsina
- Haziƙan jami'an tsaron sun samu nasarar bayan sun fatata da ƴan bindiga a lokuta daban-daban a ƙaramar hukumar Malumfashi
- DPO na ƴan sandan Malumfashi ya jagoranci tawagar da ta fafata da ƴan bindigan bayan an samu rahoto kan harin da suka kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Jami'an tsaro sun samu nasarar daƙile hare-hare guda biyu da wasu ƴan bindiga suka kai a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a ranar 11 ga watan Afrilu, 2025, a yankunan Malumfashi da Agagiwa, cikin jihar Katsina.

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an tsaro sun samu nasara kan ƴan bindiga
Nasarar jami'an tsaron ta zo ne sakamakon shirin tsaro da haɗin gwiwar da hukumomi suka yi domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Majiyoyi sun bayyana cewa da misalin ƙarfe 9:30 na dare, wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a ƙauyen Fanisau, wanda ke ƙaramar hukumar Malumfashi.
Majiyoyin sun ce, babban jami’in ƴan sanda na Malumfashi (DPO), ya jagoranci wata tawagar sintiri inda suka yi arangama da ƴan bindigan.
Bayan musayar wuta mai tsanani, an tilasta wa ƴan ta’addan janyewa daga ƙauyen, inda suka tsere ɗauke da raunuka.
Bayan wannan arangama, da misalin karfe 10:00 na dare, an samu wani kira na neman agajin gaggawa daga ƙauyen Agagiwa.
Kiran ya nuna cewa wasu ƴan bindiga sun tare hanyar Malumfashi zuwa Funtua kuma sun buɗe wuta kan wani direban mota da ke wucewa.
Ƴan sanda sun kai agajin gaggawa a Katsina

Asali: Twitter
Bayan samun wannan rahoto, DPO ya aika da wata motar yaƙi mai sulke, zuwa wajen da lamarin ya faru.
Jami’an tsaro sun fafata da ƴan bindigan, kuma bayan musayar wuta sun yi galaba a kansu, lamarin da ya tilasta musu guduwa daga yankin.
Rahotanni sun nuna cewa babu wanda ya rasa ransa daga ɓangaren jami’an tsaro ko fararen hula.
An kuma tabbatar da cewa rundunar tsaron na ci gaba da sintiri a yankunan domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana duk wata yunƙurin sake kai hari.
Al’umma a waɗannan yankuna sun nuna godiya ga hukumomin tsaro bisa wannan gagarumar nasara, tare da roƙon gwamnati da ta kara tura ƙarin jami’ai da kayan aiki domin ɗorewar zaman lafiya.
Jami'an tsaro sun yi ƙoƙari
Yusuf Ahmad ƴa shaidawa Legit Hausa cewa jami'an tsaron sun yi namijin ƙoƙari wajen fatattakar ƴan bindigan.
"Gaskiya sun yi ƙoƙari sosai kuma sun cancanci a yaba musu kan nasarar da suka samu kan ƴan bindiga."
"Muna yi musu addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara kan aikin da suke yi na samar da tsaro."
- Yusuf Ahmad
Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Dandume ta jihar Katsina.
Miyagun ƴan bindigan ɗauke da makamai sun hallaka mutum huɗu a harin da suka kai a ƙauyen Maikuma na ƙaramar hukumar.
Tawagar ƴan bindigan sun kuma yi awon gaba da aƙalla mutane 43 a harin ta'addancin da suka kai a ƙauyen.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng