Abin da Tawagar Kano Ta Fadawa Hausawan Edo bayan Ɗauke Kwamishinan Ƴan Sanda

Abin da Tawagar Kano Ta Fadawa Hausawan Edo bayan Ɗauke Kwamishinan Ƴan Sanda

  • Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tabbatar da ’yan Arewa da ke zaune a Edo suna cikin aminci da kwanciyar hankali
  • Gwarzo ya bayyana haka ne bayan dawowarsa daga ziyarar tabbatar da zaman lafiya da kuma duba lamarin kisan da ya faru a garin Uromi
  • Ya yabawa gwamnatin Edo saboda matakin da ta dauka na rusa kungiyar ƴan sa-kai, kama mutum 14 da kuma canja kwamishinan ’yan sanda
  • Mataimakin gwamnan na Kano ya bayyana cewa an mika rahoto ga Gwamnan Edo, wanda ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mamatan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya karantarwa yan Arewa mazauna jihar Edo hankali.

Gwarzo ya tabbatar da cewa ’yan Arewa da ke zaune a jihar Edo suna cikin tsaro da aminci a yanzu.

Kara karanta wannan

Kisan Hausawa: Halin da ake ciki bayan wakilan gwamnatin Kano sun isa Edo

Gwamnatin Kano ta kwantarwa Hausawan Edo hankali
Gwamnatin Kano ya ba da tabbacin samun zaman lafiya ga Hausawan Edo. Hoto: HE Sen. Monday Okpebholo.
Asali: Facebook

Edo: Yadda Hausawa suka karbi tawagar Kano

Gwarzo ya bayyana hakan ne bayan dawowarsa daga ziyara a Edo da kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar sakamakon rikicin da ya faru, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga manema labarai a Kano, Gwarzo ya ce ziyarar ta biyo bayan taziyyar Gwamna Monday Okpebholo zuwa Bunkure a Kano.

Gwarzo ya bayyana cewa tawagar ta kai ziyara wurin da lamarin ya faru a Uromi, jihar Edo, inda suka samu kyakkyawar tarba daga shugabanni.

Ya ce tarbar da suka samu ta ba su mamaki, kasancewar taron ya cika da jama’a musamman ’yan Arewa da suka nuna godiya da farin ciki.

A cewarsa:

"Mun gana da sarkin masarautar Uromi da manyan hakimansa, Gwamnan jihar Edo da kansa ya raka mu wurin da abin ya faru.
"Zuwa wurin ya dauki kusan sa’o’i biyu daga Benin, amma tarbar da muka samu da yawan jama’a ya burge mu matuka."

Kara karanta wannan

Bayan zuwan tawagar Kano, Okpebholo ya fadi yadda tinubu ya ji kan kisan ƴan Arewa

Gwarzo ya yabawa gwamnan Edo kan matakin da ya dauka
Gwamnatin Kano ta tabbatarwa Hausawan Edo kwanciyar hankali bayan kisan ƴan Arewa a jihar. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Asali: Twitter

Kisan Hausawa: Gwarzo ya yabawa gwamnan Edo

Mataimakin gwamnan ya yaba da matakin da gwamnatin Edo ta dauka na rusa kungiyar ƴan sa-kai da ake zargi da hannu a kisan da kuma kama mutane 14.

Ya ce:

"An sauya kwamishinan ’yan sandan jihar Edo saboda lamarin, alamar cewa gwamnati tana daukar lamarin da matukar muhimmanci."

Ya kara da cewa jihar Kano ta rubuta cikakken rahoto kan wadanda abin ya shafa da asarar dukiyoyin da aka yi a rikicin, cewar Tribune.

Ya bayyana cewa an mikawa Gwamnan Edo rahoton, wanda ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata.

Gwarzo ya jaddada cewa adalci ne babban abin da gwamnatin Kano ke nema tare da kare hakkin kowa na zama a ko ina cikin Najeriya.

Ya kuma tabbatar da cewa mutane 26 ne suka tsira daga harin, yawancin su daga kananan hukumomi guda biyar na jihar Kano.

Kara karanta wannan

Bayan fara tambayoyi, Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo da aka hallaka Hausawa

Tawagar Kano ta isa Edo bayan kisan Hausawa

Kun ji cewa tawagar gwamnatin Kano karkashin mataimakin gwamna, Abdulsalam Aminu Gwarzo ta isa zuwa jihar Edo.

Tawagar ta je Edo ne domin duba halin da ake ciki bayan kisan ƴan Arewa 16 da aka yi a ƙarshen watan Maris din 2025.

Hakan ya biyo bayan kisan gilla da aka yi wa wasu Hausawa 16 da ke hanyarsu ta dawowa daga Port Harcourt zuwa Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel