'Gwamnati Ta San Komai,' Dalung Ya Zargi Gwamnati da Nuku Nuku kan Boko Haram

'Gwamnati Ta San Komai,' Dalung Ya Zargi Gwamnati da Nuku Nuku kan Boko Haram

  • Minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Solomon Dalung ya ce gwamnati tana kauce wa gaskiya game da kungiyar masu aikata laifi a Filato
  • Tsohon ministan wasanni ya ce yaduwar kungiyoyin masu aikata laifi a Najeriya ya samo asali ne daga fitar da Boko Haram daga Arewa maso Gabas
  • Ya bayyana cewa 'yan ta'addan da ake kama wa suna bayar da cikakkun bayanai a kan wadanda ke daukar nauyin mugayen ayyukansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Plateau – Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung ya ce yaduwar kungiyoyin masu aikata laifi a fadin Najeriya na da alaka da yaki da ta'addanci a Arewa maso Gabas.

Dalung ya ce fitar da Boko Haram daga Arewa maso Gabas ya haifar da karuwar ayyukan ta’addanci da sace-sacen mutane a Arewa maso Yamma, Filato, da sauran wurare.

Kara karanta wannan

Jihohin Arewa 6 sun koka kan ware su a shirin noman Tinubu na dala miliyan 530

Dalung
Solomon Dalung ya zargi gwamnati da boye gaskiya kan rashin tsaro Hoto: Bayo Onanuga/Solomon Dalung
Asali: Facebook

The Cable ta ruwaito tsohon Ministan ya ce abin da ya fara a matsayin matsalar cikin gida yanzu ya zama wata hadaddiyar kungiyar laifi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalung ya kara da cewa sace-sacen mutane don neman kudaden fansa ya zama wata hanyar bunkasa tattalin arzikin wasu a siyasance.

Solomon Dalung ya fadi masu morar ta'addanci

Tsohon Ministan wasannin ya bayyana wadansu da ke da burin samun filaye masu arzikin ma'adanai ne ke mara wa ta'addancin da ake fuskanta baya.

Ya ce:

"An yi kona kabilu na asali da ke zaune a yankunan don kwace gonakinsu wadanda ke dauke da arzikin ma'adanai masu yawa, sannan kuma akwai masu daukar nauyin wannan laifi, wadanda ke sha'awar wadannan ma'adanai."

Boko Haram: An caccaki gwamnati kan ta’addancin Filato

Dalung ya kara da cewa jihar Filato, wacce aka sani da hakar ma'adanai tsawon shekaru, na daya daga cikin tushen arziki, amma gwamnati ba ta ba yankin kulawa yadda ya kamata ba.

Kara karanta wannan

'Ba mu karyata Zulum ba,' Gwamnati ta yi gyara kan batun dawowar Boko Haram

Dalung ya kuma zargi gwamnati da rashin bayyana gaskiya game da asalinsu kungiyoyin dake aikata laifuffuka a yankin.

Filato
Gwamnan Filato, Caleb Muftwang Hoto: Caleb Muftwang
Asali: Facebook

Ya tabbatar da cewa wadanda jami'an tsaro suka kama da laifuffukan suna bayar da bayanai game da masu daukar nauyinsu.

Ya tuna da wani bincike na talabijin inda wani 'dan ta'adda ya bayyana cewa bindigogin da suke amfani da su an aro su daga shugabanninsu, sannan ya bayyana cikakkun bayanai kan yadda ake rarraba kudaden fansa.

Dalung ya ce:

"Lokacin da aka tambaye shi ‘nawa kuka tara a matsayin kudin fansa?’, sai ya ce mun tara N100m. Na wa aka ba ka?’, sai ya ce N200,000," in ji Dalung.

Yadda za a magance ta’addanci a Arewa

A cikin tattaunawarsa da Legit, tsohon kwamandan rundunar JTF, Dr. Isma’il Tanko Wudilawa, ya bayyana cewa dole ne a rika hukunta wadanda ake kama da laifi idan ana so a magance ta’addanci a Arewa.

Ya ce:

Kara karanta wannan

An fara mantawa: Lauya ya taso da maganar kisan Hausawa a Edo da tambayoyi 10

"Makaman da ‘yan ta’addan ke amfani da su ba irin wadanda gwamnatin Najeriya ta saya ne. Su na da manyan makaman da ko jami'an gwamnatin Najeriya ba su mallaka ba."

Dr. Wudilawa yana ganin akwai bukatar a kara inganta tsaro ta hanyar sanya CCTV a yankunan da aka san 'yan ta'adda na aikinsu, sannan a tanadi masu sa ido na musamman a kan kyamarorin.

Ya kuma shawartar yankunan da ke fama da rashin tsaro, da su gaggauta sanar da hukumomi idan sun ga abin da hankalinsu bai kwantra da shi ba.

Gwamnati ya magantu kan batun Boko Haram

A baya, kun samu labarin cewa Ofishin Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a ya ce an juya martanin Mohammed Idris kan damuwar Gwamnan Borno na dawowar Boko Haram.

A cikin rahoton da aka fitar, gwamna Babagana Zulum ya bayyana damuwarsa kan yadda mayakan Boko Haram ke kara karfi, suna fatattakar jama'a daga garuruwansu, suna zama.

Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya ba ta yi watsi da kukan gwamnan ba, sai dai ya bayyana cewa an fitar gwamnati tana iya bakin kokarinta wajen kawar da matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel