Bayan Mako 1 Yana Shiru, Buhari Ya Magantu kan Rasuwar Idris Dutsen Tanshi

Bayan Mako 1 Yana Shiru, Buhari Ya Magantu kan Rasuwar Idris Dutsen Tanshi

  • Muhammadu Buhari y bayyana alhini kan rasuwar Sheikh Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi, yana mai jajantawa iyalansa da al’ummar jihar Bauchi
  • Tsohon shugaban kasar ya ce marigayin malami ne na musamman da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da addini da taimakon marasa galihu
  • Sanarwar Buhari ta bayyana cewa Sheikh Idris Dutsen Tanshi mutum ne da ya shahara wajen yaye jahilci da karantar da Musulunci a Najeriya baki daya
  • Buhari ya roki Allah ya gafarta wa marigayin, ya saka masa da gidan Aljanna, tare da jajantawa dalibansa da dukan al’ummar Musulmi a Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana bayan rasuwar Sheikh Abdul'aziz Idris Dutsen Tanshi.

Buhari ya jajantawa iyalan marigayin kan babban rashin da aka yi da cewa ba iya gidansu ba har ma jihar da Najeriya baki daya sun yi rashi.

Kara karanta wannan

Ana cikin karbar ta'azziya, iyalan Dutsen Tanshi sun sake gargadi kan wasiyyarsa

Buhari ya mika ta'aziyya bayan rasuwar Malam Idris Dutsen Tanshi
Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan marigayi Sheikh Idris Dutsen Tanshi. Hoto: @Buharisallau1.
Asali: Twitter

Wannan na cikin wata sanarwa da Buhari ya sanyawa hannu wanda tsohon hadiminsa, Buhari Sallau ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanar da rasuwar Idris Dutsen Tanshi

Hakan ya biyo bayan rasuwar malamin addinin, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi a jihar Bauchi.

Majiyoyi sun ce Sheikh Idris Abdulaziz ya rasu ne cikin daren ranar Juma'a, 3 ga Afrilu, 2025 bayan shafe lokaci mai tsawo yana jinya.

Mutuwar malamin ya sanya al'ummar Musulmi cikin tsananin jimami yayin da suke yabawa da kokarinsa a koyarwar addini.

A karshe, Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Malam Idris Dutsen Tanshi
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaɗu da samun labarin rasuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi. Hoto: Dutsen Tanshi Majlis Bauchi.
Asali: Facebook

Martanin Buhari kan rasuwar Malam Dutsen Tanshi

A cikin, sanarwar Buhari ya bayyana marigayin a matsayin fitaccen malami na musamman wanda ya ba da gudunmawa sosai.

Buhari ya bayyana irin sadaukar da rasuwarsa da marigayin ya yi domin ganin al'umma sun rabauta.

Daga bisani, ya ce marigayi Malam Idris Dutsen Tanshi ya karar da rayuwarsa wurin tabbatar da taimakon marasa karfi da al'umma baki daya.

Kara karanta wannan

Abin da ya faru tsakanin daliban Dutsen Tanshi da gwamnan Bauchi wajen ta'aziyya

A cikin sanarwar, Buhari ya ce:

"Da ni da iyalaina mun kadu da samun labarin rasuwar Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.
"Malamin ya kasance na musamman wanda ya ba da gudunmawa sosai kuma marar misaltuwa ga addinin Musulunci.
"A tsawon rayuwarsa, ya mayar da hankali wurin koyar da addini kuma ya kasance sanannen mutum mai taimakawa al'umma da marasa karfi.

Daga bisani, Buhari ya yi ta'aziyya ga dalibansa da sauran al'ummar Musulmi a fadin Najeriya baki daya.

Ya kuma yi masa addu'a ta musamman domin samun rahama da dacewa a lahira.

"Ina jajantawa sauran iyalansa, dalibai da al'ummar Musulmi a fadin Najeriya.
"Allah ya gafarta masa ya sanya shi gidan aljannar Firdausi, Ameen."

Tinubu ya jajanta kan rasuwar Malam Idris

A baya, mun ba ku labarin cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyyar rasuwar fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Abdul'Aziz Idris Dutsen Tanshi.

Kara karanta wannan

Atiku da shugaban SDP sun ziyarci Aisha Buhari bayan an mata rashi

Tinubu ya bayyana cewa aikin da malamin ya yi wajen yaƙi da tsattsauran ra'ayi da ta'addanci a Arewa maso Gabas ya nuna irin jajircewarsa.

Shugaban ya roki Allah ya gafarta wa Sheikh Dutsen Tanshi kuma ya ba iyalansa da almajiransa haƙurin jure wannan rashi da aka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng