Sabuwar Wakar Caccakar Tinubu Ta Tayar da Kura a Najeriya
- Kungiyar Amnesty International ta caccaki haramta wakar Eedris Abdulkareem da NBC ta yi, ta ce matakin ya saba wa doka
- A karkashin haka ne Amnesty ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya tilastawa hukumar NBC ta janye matakin haramta sanya wakar
- Kungiyar ta bayyana cewa lamarin zai iya haifar da matsin lamba ga kafafen watsa labarai da kuma tsoratar da 'yan Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce matakin NBC na haramta sabuwar waƙar Eedris Abdulkareem ta sukar Bola Tinubu ya saba doka.
A cikin wata sanarwa da Amnesty ta fitar a ranar Alhamis, kungiyar ta ce haramta wakar da ke sukar gwamnati da nuna halin rayuwa da ƙuncin tattalin arziki abin damuwa ne matuka.

Asali: Instagram
A cikin sakon da ta wallafa a X, kungiyar ta ce haramta wakar barazana ne ga 'yancin fadin albarkacin baki a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amnesty ta caccaki NBC da gwamnati
Amnesty ta bayyana cewa wannan mataki ya kara nuna yadda gwamnati ke tsoratar da masu sukar ta, musamman a karkashin mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Kungiyar ta ce:
“Shigar da wakar cikin jerin abubuwan da ba za a watsa ba saboda sukar gwamnati tamkar amfani ne da iko ba bisa ka’ida ba.”
Kungiyar ta kuma bukaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta bada umarnin janye haramcin, tana mai cewa hakan ne kadai zai nuna biyayya ga kare hakkin bil’adama.
Tasirin hana saka wakar a Najeriya
A cewar Amnesty, wannan yunkuri na NBC zai iya haifar da mummunan tasiri ga masu fasaha, kafafen yada labarai da kuma 'yancin 'yan kasa na bayyana ra’ayinsu cikin lumana.
Punch ta wallafa cewa kungiyar ta ce:
“Haramcin zai haifar da tsoro da toshe basirar masu fasaha a Najeriya."
Amnesty ta bayyana cewa matakin NBC ya sabawa yarjejeniyoyin kasa da kasa da na Afirka da Najeriya ta rattaba wa hannu da ke kare ’yancin fadar albarkacin baki da walwalar masu fasaha.

Asali: Facebook
Bukatar sake duba dokokin NBC
Kungiyar ta bukaci a yi sauye-sauye cikin gaggawa a tsarin dokokin NBC da ake amfani da su wajen danne kafafen yada labarai da masu sukar gwamnati.
Kungiyar ta ce:
“Haramcin ya sake bude batun sauya dokokin NBC da ake amfani da su wajen danne walwala da ‘yancin bayyana ra’ayi a Najeriya,”
Amnesty ta kammala da jan hankalin gwamnati cewa idan aka bar wannan mataki haka, zai haifar da sabuwar hanya ta danniya da tsoratar da masu bayyana korafi a fili.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, NBC ba ta mayar da martani ba, haka kuma ba a ji ta bakin Shugaba Tinubu kan lamarin ba.
Jihohin Arewa 6 sun mika korafi ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa Sanatoci da 'yan majalisun tarayya da suka fito daga Arewa maso Gabas sun koka kan wani shiri da Bola Tinubu ya kawo.
Sanata Danjuma Goje da ya yi magana a madadin 'yan majalisun ya ce an ware makudan kudi domin noma amma ba a saka yankinsu a ciki ba.
A karkashin haka Sanata Goje ya bukaci a sake duba lamarin tare da sanya jihohin Arewa maso Gabas kasancewar suna da kasar noma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng