Kisan Hausawa: Halin da ake ciki bayan Wakilan Gwamnatin Kano Sun Isa Edo
- Gwamnatin tarayya tare da ta Edo sun kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin kisan mutane 16 da aka yi a Uromi
- Baya ga haka, gwamna Okpebholo ya karɓi rahoton kwamitin Kano daga Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu A. Gwarzo
- An bayyana cewa Shugaba Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru ba, kuma ya kuduri aniyar ganin an hukunta masu hannu a laifin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da ta jiharsa sun kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin kisan Hausawa 16.
Ana zargin cewa mutanen gari ne suka kashe wasu mafarauta 'yan Arewa a garin Uromi a jihar Edo.

Asali: Twitter
Vanguard ta rahoto cewa gwamnan Edo ya fadi haka ne lokacin da ya karɓi wata babbar tawaga daga jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Gwamna, Aminu Gwarzo.

Kara karanta wannan
Bayan zuwan tawagar Kano, Okpebholo ya fadi yadda tinubu ya ji kan kisan ƴan Arewa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Gwarzo ya miƙa rahoton kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa domin tantance waɗanda suka tsira, waɗanda aka kashe da kuma ‘yan uwansu na kusa.
Aikin da kwamitin binciken kisan Hausawa zai yi
Gwamnan Edo ya ce kwamitin da aka kafa zai binciko musabbabin kisan tare da samar da mafita mai dorewa.
Gwamna Okpebholo ya ƙara da cewa rahoton da Kano ta gabatar zai taimaka matuka ga aikin kwamitin.
Tinubu ya nuna damuwar kisan Hausawa a Edo
Gwamna Okpebholo ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu yana cikin damuwa da abin da ya faru a Uromi, kuma yana son a tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga kowa a faɗin ƙasar nan.
Rahoton Channels TV ya nuna cewa gwamna Monday Okpebholo ya ce:
“Mummunan lamarin ya bude mana idanu kuma mun kuduri aniyar gyara abubuwa da dama domin kyautata rayuwar ‘yan ƙasa.”

Kara karanta wannan
Bayan fara tambayoyi, Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo da aka hallaka Hausawa
Edo na kaunar zaman lafiya da hadin kai
Gwamna Okpebholo ya ce jihar Edo tana ƙaunar zaman lafiya, kuma tana girmama kowa da ke zaune cikinta, ko daga ina ya fito.
Ya jaddada cewa Edo da Kano na da kyakkyawar alaka musamman a fannin kasuwanci da masana’antu.
Okpebholo ya ce:
“Muna da tarihin alaka mai kyau da jihar Kano. A wannan lokaci mai cike da ƙalubale, muna bukatar fahimta da haɗin kai tsakanin jihohin mu.”
Binciken da jihar Kano ta yi kan lamarin
Da yake jawabi, Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo, ya gode wa Gwamna Okpebholo bisa ziyarar da ya kai Kano a baya domin jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Ya bayyana cewa:
“Gwamnanmu ya kafa kwamitin tantance sunaye da adadin mutanen da suka mutu da waɗanda suka tsira.
Mun kammala binciken kuma mun kawo rahoton ga Mai Girma Gwamna.”
Aminu Gwarzo ya ce mutane 16 daga ƙananan hukumomi biyar na Kano ne suka rasa rayukansu a kisan, kuma suna fatan ganin adalci ya yi aiki cikin gaskiya da bayyani.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Kano tana da cikakken tabbaci kan alkawarin da Gwamnan Edo ya dauka na ganin an hukunta masu hannu a kisan tare da bayar da diyya.

Asali: Facebook
Tambayoyi 10 kan kisan Hausawa a Edo
A wani rahoton, kun ji cewa lauya mai kare hakkin dan Adam, Abba Hikima ya yi tambayoyi 10 kan kisan Hausawa a Edo.
Barista Abba Hikima ya bukaci sanin adadin wadanda aka kama da kuma halin da ake ciki game da binciken da ake gudanarwa.
Abba Hikima ya bayyana cewa komai muhimmancin lamari a haka yake wucewa a Najeriya ba tare da jin halin da ake ciki ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng