Me Ya Yi Zafi: Jam'iyyar APC Ta Fadi Dalilin Rufe Hedkwatarta Ta Kasa
- Mutuwar dakaraktan gudanarwa na APC, Alhaji AbdulRauf Adeniji, ta girgiza jam'iyya mai mulki a Najeriya
- APC ta ɗauki matakin rufe hedkwatarta ta ƙasa da ke Abuja domin nuna alhininta kan kisan gillar da aka yi wa daraktan
- Marigayi Alhaji AbdulRauf Adeniji ya rasa ransa ne a hannun masu garkuwa da mutane waɗanda suka sace shi duk da an ba su kuɗin fansa
- Jam'iyyar ta ce rufe hedkwatarta ta ƙasa zai kasance ne har zuwa ranar Litinin, 14 ga watan Afirilun 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta rufe hedkwatarta ta ƙasa da ke Abuja, wadda aka fi sani da Buhari House.
Jam'iyyar APC ta ɗauki matakin rufe hedkwatarta ta ƙasa ne sakamakon kisan gillan da aka yi wa daraktan gudanarwa na jam’iyyar, Alhaji AbdulRauf Adeniji.

Asali: Twitter
Jam’iyyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe daraktan jam'iyyar APC
Rahotanni sun nuna cewa marigayin wanda ya kwashe tsawon makonni a hannun masu garkuwa da mutane, an kashe shi a watan da ya gabata.
Marigayin daraktan an sace shi ne watanni biyu da suka wuce kuma an kashe shi duk da cewa an biya kudin fansa har Naira miliyan 50 domin a sako shi.
An bayyana cewa Alhaji AbdulRauf Adeniji ya kasance a cikin sahun gaba wajen masu jagoranci a ofishin jam’iyyar APC na ƙasa, kuma ya shafe shekaru yana aiki tuƙuru domin nasarar jam'iyyar.
Sanarwar ta ce rufewar za ta kasance har zuwa ranar Litinin, 14 ga watan Afrilu, 2025, domin bayar da dama ga ma’aikata da mambobi su yi juyayi da addu’a ga marigayin da iyalansa.
Jam’iyyar ta shawarci dukkan ma’aikatanta da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin tunani mai zurfi da kuma addu’a don marigayi AbdulRauf Adeniji, iyalansa da sauran masoyansa da suka rasa shi.

Kara karanta wannan
Atiku, Obi da El Rufai na shirin haɗewa, Tinubu ya bude kofar kayar da shi a 2027
Haka kuma, an sanar da buɗe littafin ta’aziyya a cikin harabar hedkwatar jam’iyyar domin girmama marigayin tare da bai wa mambobi da abokan aiki damar rubuta saƙonnin ta’aziyya cikin girmamawa.
Meyasa aka rufe hedkwatar APC?
Sanarwar ta bayyana cewa:
"Sakataren jam’iyya na ƙasa ya amince da rufe hedkwatar jam'iyya daga duk wasu ayyuka nan take har zuwa ranar Litinin, 14 ga watan Afrilu, 2025.
"Wannan mataki ya biyo bayan samun labarin rasuwar daraktan gudanarwa, Marigayi Hon. AbdulRauf Adekunle Adeniji, wanda ya kasance mutum mai gaskiya da ƙwazo."
Buhari ya yi wa gwamnonin APC nasiha
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya labule da gwamnonin jam'iyyar APC a gidansa da ke Kaduna.
Tsohon shugaban ƙasan ya jawo hankalinsu kan su riƙa fifita buƙatan mutanen da suke wakilta maimakon na su na ƙashin kansu.
Buhari ya tunatar da su cewa shugabanci cike yake da ƙalubale amma yana ba da damar yin abubuwan da suka dace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng