Bayan Zuwan Tawagar Kano, Okpebholo Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Ji kan Kisan Ƴan Arewa

Bayan Zuwan Tawagar Kano, Okpebholo Ya Fadi Yadda Tinubu Ya Ji kan Kisan Ƴan Arewa

  • Gwamnatin tarayya da ta Edo sun kafa kwamitin bincike don gano musabbabin kisan matafiya 16 'yan Kano a Uromi, jihar Edo
  • Gwamna Monday Okpebholo ya ce Shugaba Bola Tinubu bai ji dadin lamarin ba, yana so a samar da zaman lafiya da tsaro
  • Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya kai rahoto ga gwamnan Edo game da adadin mutanen da suka mutu da wadanda suka tsira
  • Kwamitin daga Kano ya tabbatar mutane 16 daga kananan hukumomi 5 na Kano ne suka mutu, kuma ana sa ran a tabbatar da adalci gare su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Benin-City, Edo - Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo ya bayyana shirin da suke yi kan kisan Hausawa a Uromi.

Okpebholo ya ce gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar jihar Edo sun kafa kwamitin bincike kan kisan matafiya 16 a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan fara tambayoyi, Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo da aka hallaka Hausawa

Gwamnan Edo ya yi wa al'ummar Kano alkawarin bi musu kadu
Gwamna Okpebholo ya ce an kafa kwamiti na musamman kan kisan Hausawa a Edo. Hoto: HE Sen. Monday Okpebholo.
Asali: Facebook

Uromi: Shirin Tinubu da gwamnatin Edo

Okpebholo ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi tawagar jihar Kano mai jagorancin mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya fadi yadda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan lamarin da ya faru.

Okpebholo ya ce:

“Shugaba Bola Tinubu bai ji dadin abin da ya faru a Uromi ba, kuma yana son ganin an kare rayuka da dukiya.”
“Wannan abin da ya faru ya bude mana ido domin magance matsalolin da ke addabar kasar nan don samun kyakkyawan rayuwa.”
“Shugaban kasa yana son ganin an warware wannan matsala, mun kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin lamarin da kawo mafita.”
“Rahoton da kuka kawo zai taimaka mana, za mu sanar da jama’a abubuwan da kwamitin bincike ke yi a fili.”
Gwamnatin Edo ta dauko hanyar shawo kan matsalar kisan Hausawa a Uromi
Gwamna Monday Okpebholo ya hada kai Bola Tinubu bayan kisan Hausawa a Edo. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Asali: Twitter

Edo: Gwamnatin Kano ta yabawa Okpebholo

A bangarensa, Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya gode wa Gwamna Okpebholo kan kokarinsa.

Kara karanta wannan

'Mun yi kuskure,' Gwamnatin Tinubu ta ba da hakuri kan maganar nada mukamai

Gwarzo musamman ya yabe shi saboda ziyarar da ya kai Kano dangane da harin da aka kai a Uromi.

Gwarzo ya ce:

"Gwamnan Kano ya kafa kwamitin tantance sunaye da adadin wadanda suka mutu da wadanda suka tsira daga harin da aka kai.”
“Mun kammala bincike kuma mun fito da rahoto wanda muka kawo muku domin mika shi gare ku a hukumance.”
“Ka yi alkawarin cewa za a tabbatar da adalci, kuma muna da tabbacin za ka cika alkawarin nan, Gwamna.”

Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin gwamnan Edo, Dennis Idahosa, da shugaban majalisar dokokin jihar, Hon Blessing Agbebaku, da jami’an tsaro.

Gwamnan Edo da tawagar jihar Kano sun kuma ziyarci Uromi inda suka gana da mambobin al’ummar Hausawa da ke yankin domin jaje.

Tawagar gwamnatin Kano ta isa Edo

A baya, kun ji cewa mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci kwamiti zuwa jihar Edo.

Kara karanta wannan

Uromi: An barke da zanga zanga bayan matakin 'yan sanda da aka kashe Hausawa

Gwarzo ya jagoranci kwamitin ne domin binciken kashe-kashen da suka faru a kauyen Uromi da ke jihar a karshen watan Maris.

Kwamitin ya kunshi manyan jami’ai ciki har da Sarkin Rano, da kwamishinoni daga ma’aikatun addini, kananan hukumomi, da harkokin mata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel