Duk da Hare Haren Boko Haram, Gwamnati Za Ta Shigar da Tubabbun 'Yan Ta'adda cikin Al'umma

Duk da Hare Haren Boko Haram, Gwamnati Za Ta Shigar da Tubabbun 'Yan Ta'adda cikin Al'umma

  • Gwamnatin jihar Yobe ta gamsu da shirin sauya tunani da gyara halayen wasu tsofaffin ƴan ta'addan Boko Haram da suka tuba
  • Ta bayyana cewa ta shirya shigar da tubabbun ƴan ta'addan na Boko Haram cikin al'umma domin su ci gaba da gudanar da rayuwarsa
  • Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa akwai da dama daga cikin ƴan ta'addan da ba da son ransu suka shiga harkar ta'addanci ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta bayyana shirinta kan tubabbun ƴan ta'addan boko Haram.

Gwamnatin ta ce ta shirya shigar da tsofaffin ƴan ta'addan waɗanda suka halarci shirin sauya tunani da gyaran hali cikin al'umma.

Gwamna Mai Mala Buni
Gwamnatin Yobe ta gamsu da tubar wasu 'yan Boko Haram Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Gwamna Mai Mala Buni ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Damaturu, yayin da ya karɓi tawagar OPSC ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Mummunan fada ya barke a tsakanin 'yan bindiga, miyagu sun tafi barzahu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sauya tunanin ƴan Boko Haram

Shirin sauya tunanin ƴan ta'addan na Boko Haram dai na gudana ne a ƙarƙashin Operation Safe Corridor (OPSC)

Gwamna Buni, wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya wakilta, ya bayyana wannan ziyara a matsayin wata damar yin haɗin gwiwa da tsara dabaru tsakanin gwamnatin jihar da hukumomin tsaro.

Ya bayyana yadda rikicin Boko Haram da ya ɗauki fiye da shekaru 15 ya hallaka dubban rayuka a jihar Yobe, ya lalata dukiyoyin gwamnati da na masu zaman kansu, tare da raba dubban mutane da muhallansu.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta gane cewa ba dukan mambobin ƙungiyar ta'addancin ne suka shiga da son ransu ba, yana mai cewa amfani da dabarar sulhu da fahimtar juna na iya ceto waɗanda suka nuna nadama.

“Muna da yaƙinin cewa wasu daga cikinsu an tilasta musu shiga ƙungiyar ko kuma an rinjaye su ta hanyar cusa musu mummunar aƙida."

Kara karanta wannan

Ana batun hadaka, shugaba a APC ya fadi tagomashin da Arewa ta samu a mulkin Tinubu

"Idan aka ci gaba da jajircewa, suna iya tuba, a gyara su, sannan su koma rayuwa mai kyau a matsayin ƴan ƙasa nagari."

- Gwamna Mai Mala Buni

Gwamna Mai Mala Buni
Gwamnatin Yobe za ta shigar da tubabbun Boko Haram cikin al'umma Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Yaushe za a shigar da su cikin al'umma

Ya ƙara da cewa akwai tsofaffin yan Boko Haram 390 da suka tuba, ciki har da ƴan asalin jihar Yobe 54, da za su kammala shirin sauya musu tunani daga ranar 14 zuwa 19 ga watan Afrilun 2025.

Ya ce gwamnatin jihar ta tanadi tsarin da zai taimaka wajen sake shigar da su cikin al’umma, ta hannun ma’aikatar harkokin jin ƙai.

“Ina so na tabbatar wa da Operation Safe Corridor cewa gwamnatin jihar Yobe tana da cikakken shiri na rungumar shawarwarinku da kuma aiwatar da su domin cimma burin da ake fatan samu."

- Gwamna Mai Mala Buni

A ƙarshe, Gwamna Buni ya nuna godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu saboda irin jajircewarsa wajen kawo ƙarshen ta’addanci da sauran manyan laifuka ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban.

Kara karanta wannan

'Ƴan bindiga sun kai hare-haren ramuwar gayya a Zamfara, sun yi barna

Zulum ya koka kan barnar ƴan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa kan ƙaruwar hare-haren ƴan Boko Haram.

Mai girma Gwamna Zulum ya bayyana cewa ƙaruwar hare-haren ƴan ta'addan da ake samu babban koma baya ne ga jihar.

Zulum ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa ta hanyar yin amfani da fasahar zamani domin kawo ƙarshen matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel