Rashin Imani: 'Yan Bindiga Sun Zo da Sabon Salon Ta'addanci a Katsina
- Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ramuwar gayya a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina
- Ƴan bindiga sun riƙa ajiye gawarwakin mutanen da suka kashe a ƙofar shiga ƙauyen Tafoki domin tsoratar da mutane
- Harin ramuwar gayya na zuwa ne bayan mutanen ƙauyen sun hallaka wani tantirin jagoran ƴan bindiga a wani artabu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kai mummunan harin ramuwar gayya a ƙauyen Tafoki da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Miyagun ƴan bindigan sun ajiye gawarwaki da dama a bakin ƙofar ƙauyen domin razana jama'a.

Asali: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka yi ta'asa a Katsina
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ƴan bindigan, waɗanda mafi yawansu matasa ne tsakanin shekaru 20 zuwa sama, sun iso ƙauyen ne a ranar 9 ga Afrilu, 2025.
Suna isowa, sai suka ajiye gawarwakin wasu mutanen da suka kashe a bakin hanyar shiga ƙauyen, wanda hakan ya jefa mazauna ƙauyen cikin tsananin fargaba da ruɗani.
Rahotanni sun bayyana cewa harin na ramuwar gayya ne saboda kashe wasu ƴan bindiga guda uku da mazauna ƙauyen suka yi a watan Fabrairun 2025.
An kashe miyagun ne lokacin da ƴan bindiga suka yi yunƙurin kai hari a ƙauyen amma suka fuskanci turjiya daga mutanen ƙauyen.
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe a wancan lokacin shi ne Goje, wani shahararren tantirin jagoran ƴan bindiga, wanda ya jagoranci harin da bai yi nasara ba.
Bayan wannan al’amari, rahotanni sun ƙara bayyana cewa ƴan bindigan sun fara kama mazauna ƙauyen, inda suke ɗaure hannuwansu a bayansu, sannan suna harbin su a kai, tare da dawowa da gawarwakin don ajiye su a bakin ƙofar ƙauyen.
Ƴan bindiga sun jefa mutane cikin firgici
Wannan mummunan aikin ta'addancin na ƴan bindiga ya ƙara nuna irin tsabagen zaluncinsu da rashin imanin da suke da shi.

Asali: Twitter
Yayin da iyalai ke cikin jimami da alhini, suna ɗaukar gawarwakin ƴan uwansu da suka fara wari da lalacewa.
Wasu daga cikin su ba su ma gane ƴan uwansu ba saboda yadda gawarwakin suka lalace.
Al’ummar kauyen Tafoki sun shiga cikin mawuyacin hali tare da firgici sakamakon wannan ta’addanci.
A yanzu haka, suna rayuwa cikin fargaba da dar-dar, ganin yadda ƙoƙarinsu na kare kansu daga barazanar ƴan bindiga ya jawo harin ramuwar gayya.
Ƴan bindiiga sun gwabza faɗa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ƙazamin faɗa ya barke a tsakanin ƴan bindiga masu gaba da juna a jihar Kaduna.
Mummunan faɗan na nuna ƙarfin iko ya ɓarke ne a tsakanin wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar.
Faɗan da aka daɗe ana gwabzawa ya jawo sanadiyyar tura aƙalla miyagun ƴan binɗiga a Kaduna guda 10 zuwa barzahu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng