Turji Ya Sauya Salo, an Gano Ƴan Ta'adda Na Shiga Sokoto daga Dazukan Zamfara

Turji Ya Sauya Salo, an Gano Ƴan Ta'adda Na Shiga Sokoto daga Dazukan Zamfara

  • Rahotanni sun nuna 'yan bindiga fiye da 200 sun tsere daga dazukan Zamfara zuwa yankin Isa da Sabon Birni a jihar Sokoto
  • An ce hare-haren sojoji a Danjibga da wasu dazukan Kudancin Zamfara ne suka tilasta wa 'yan bindigar guduwa daga maboyarsu
  • Rahoton ya nuna 'yan bindigar na amfani da dazukan Gusami, Rugu da Rukudawa suna shiga Dutsi har zuwa Fakai da yankin Isa
  • Ana zargin shahararren 'dan bindiga, Bello Turji, yana da hannu wajen shirya wannan sauya matsugunin tare da jagorantar komai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Majiyoyin leken asiri sun bayyana yadda wasu ƴan bindiga suke sauya mafaka a Arewa maso Yamma.

Rahotanni sun ce wasu yan bindiga suna sauya matsuguni daga dazukan Zamfara zuwa wasu yankunan Jihar Sokoto sakamakon farmakin sojoji.

Kara karanta wannan

An fara mantawa: Lauya ya taso da maganar kisan Hausawa a Edo da tambayoyi 10

Wasu daga cikin mayakan Turji na sauya dazuka a Najeriya
Ana fargabar wasu yan bindiga na barin dazukan Zamfara zuwa Sokoto. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Shafin Zagazola Makama shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X a yau Alhamis 10 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yi watsi da belin ƴan ta'adda

Wannan na zuwa ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar beli da wasu mutum hudu da ake zargi da alaka da gawurtaccen dan ta’adda, Bello Turji.

Mai shari’a Emeka Nwite ya yanke hukunci cewa za a hanzarta shari’ar mutanen hudu, tare da amincewa da bukatar gwamnati na kare shaidun.

Duk da cewa mutum takwas aka lissafa a cikin tuhume-tuhume 11 da ake yi masu, uku daga cikinsu, ciki har da Bello Turji ba su shiga hannu ba.

Bello Turji ya kai hare-hare a Sokoto

Daga bisani, dan ta'addan ya kai farmaki kan wasu manoma a garin Lugu da ke karamar hukumar Isa, a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan daliban jami'a a Kebbi cikin dare

Majiyoyi sun ce Turji na dawowa ne daga wata ziyarar Sallah da ya kai a Isa lokacin da ya kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 11.

Wasu mazauna yankin sun ce sun dade da samun labarin shirin Turji na kai ziyara zuwa gabashin Gatawa a karamar hukumar Sabon Birni.

Yadda yan bindiga ke kaura daga dazukan Zamfara zuwa Sokoto
Majiyoyi sun ce wasu mayaka da ke da alaka da Bello Turji na kaura daga wasu dazukan Zamfara zuwa Sokoto. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda yan bindiga ke kaura zuwa Sokoto

An ce hare-haren sojoji a Danjibga da Kudancin Zamfara ya tilasta wa 'yan bindiga barin maboyarsu a dazukan Zamfara zuwa Isa da Sabon Birni.

An bayyana cewa 'yan bindigar suna taruwa ne a dazukan Gusami da Rugu a Zamfara zuwa dajin Rukudawa kusa da Zurmi, suna wucewa Dutsi har zuwa Fakai da Isa.

Rahotanni sun bayyana cewa sama da 'yan bindiga 200 sun shiga yankin Isa da Sabon Birni da jihar Sokoto.

Kuma ana kyautata zaton rikakken ɗan bindiga, Bello Turji na da hannu a lamarin.

Sheikh Asada ya yi bankado batun ta'addanci

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Fitattun wawaƙa 4 a Najeriya sun mutu a mummunan hatsarin mota

Mun ba ku labarin cewa Sheikh Murtala Bello Asada ya sake tasowa da bayani kan yadda matsalar tsaro ke ƙara kamari a Arewa maso Yamma, yana kalubalantar jami'an tsaro.

Malamin ya ce yana da hujjoji da ke nuna yadda manyan 'yan bindiga ke yawo babu tsoro, inda ya bayyana sunayensu da maboyarsu.

Sheikh Asada ya zargi wasu jami'an tsaro da bayanai kan 'yan ta'adda, yana neman a fitar da gaskiya kan inda makamansu da motocinsu suka fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel