Mummunan Fada Ya Barke a Tsakanin 'Yan Bindiga, Miyagu Sun Tafi Barzahu

Mummunan Fada Ya Barke a Tsakanin 'Yan Bindiga, Miyagu Sun Tafi Barzahu

  • Ƴan bindiga masu gaba da juna sun nuna ƙwanji a tsakaninsu a ƙaramar hukumar Giwa da ke Arewacin jihar Kaduna
  • Hatsabibin ƴan bindigan sun yi mummunan artabu a tsakaninsu wanda ya jawo asarar rayukan miyagu guda 10
  • Majiyoyi sun bayyana cewa faɗan ya auku ne a Talata, 8 ga watan Afirilun 2025 a tsakanin wasu ƙauyuka guda biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wani mummunan faɗa ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga masu adawa da juna a ranar 8 ga watan Afrilu, 2025, a ƙaramar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.

Mummunan faɗan ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla ƴan bindiga guda 10 bayan sun yi musayar wuta a tsakaninsu.

'Yan bindiga sun yi fada a Kaduna
'Yan bindiga sun gwabza fada da junansu a Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X

Kara karanta wannan

"Akwai talauci a Najeriya": Peter Obi ya fadi yadda rayuwa ta sauya masa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mummunan rikicin ya sake jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali.

Yadda ƴan bindiga suka gwabza a Kaduna

Majiyoyin sirri sun bayyana cewa faɗan ƴa ɓarke ne da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, a tsakanin ƙauyukan Toroko da Awala.

Duk da cewa har yanzu ba a bayyana takamaiman musabbabin rikicin ba, alamu na nuna cewa rikicin na da nasaba da gardama kan iko a tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindigan masu ɗauke da makamai.

Shaidu da suka ga yadda lamarin ya faru sun bayyana cewa rikicin ya kasance mai tsanani, inda aka ji ƙarar harbe-harbe masu ƙarfi a cikin dazukan da ke tsakanin waɗannan ƙauyuka.

Wannan na nuni da yadda kowane ɓangare ke kokarin karɓe iko da yankin da nuna ƙarfi kan abokin gabarsa.

A cewarsu, wasu daga cikin ƴan bindigan da suka mutu sun kasance waɗanda ke yawan kai hare-hare a yankunan Arewa maso Yamma.

A halin yanzu, rikicin ya bar al’ummar yankin cikin tsoro da damuwa, ganin yadda rikice-rikice ke ƙara tsananta.

Kara karanta wannan

2027: Kungiyoyin Arewa 65,000 sun bayyana matsayarsu kan takarar Tinubu

Al’ummar yankin sun yi kira ga gwamnati da ta tura ƙarin jami’an tsaro domin samar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Jihar Kaduna dai na ɗaya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya masu fama da matsalar rashin tsaro.

Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga a Najeriya

Ƴan bindiga sun kai hare-haren ramuwar gayya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun fusata kan nasarar da jami'an tsaro suka samu ta kashe wasu manya-manyan jagororinsu a jihar Zamfara.

Hakan ya sanya tantiran miyagun suka ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar.

Ƴan bindigan a yayin hare-haren, sun hallaka mutum uku yayin da suka yi awon gaba da wasu mutane aƙalla guda 60 zuwa cikin daji.

Tsagerun sun kuma ƙona motoci tare da fasa shaguna inda suka saci kayayyaki masu tarin yawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng