'Yan Sanda Sun Cafke Mutane Sama da 100 da Suka kai Farmaki cikin Dare a Abuja
- Rundunar ‘yan sandan Abuja ta kama mutane 136 a wani samame da ta kai maboyar ‘yan fashi da sauran miyagu a unguwanni daban-daban na babban birnin tarayya
- An kai samamen ne da misalin ƙarfe 11:40 na daren Talata, inda aka kai farmaki a gine-ginen da ba a kammala ba da wuraren da ake zargi da kasancewa mafakar masu laifi
- Sun kwato makamai da tabar wiwi da wasu miyagun ƙwayoyi daga hannun waɗanda ake zargi, kuma an fara tantance su kafin gurfanar da masu laifi a gaban kotu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta fara wani sabon shiri na yaki da miyagun laifuffuka.
A karkashin shirin, ta gudanar da samame mai faɗi a cikin birnin domin kawar da baragurbin mutane daga al’umma.

Asali: Facebook
'Yan sanda sun yi kame a birnin Abuja
Rahoton da Zagazola Makama ya wallafa a X ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne da hadin gwiwar ofisoshin ‘yan sanda 13 daga sassa daban-daban na birnin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa samamen dai ya biyo bayan rahotannin sirri da aka tattara dangane da maboyar miyagu.
A cikin rahoton, an bayyana cewa aikin rundunar ya biyo bayan shirin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin babban birnin tarayya.
An kama mutane 136 a lokaci guda
A cewar majiyoyin rundunar 'yan sanda, an gudanar da samamen da misalin ƙarfe 11:40 na daren Talata, 9 ga Afrilu, 2025.
Samamen ya gudana a unguwanni da dama da suka hada da Kabusa, Garki, Wuse, Kubwa, Byazhin, Dutse Alhaji, Karu, Maitama, Zuba, Dei-Dei ‘B’, Karmo, Utako, Gwarinpa da Wuye.
Daga cikin abubuwan da aka kwato sun haɗa da adduna huɗu, ganyen tabar wiwi, da kuma wasu nau’o’in miyagun ƙwayoyi.

Kara karanta wannan
Bayan Wike ya gana da 'yan majalisa, an bijirewa kotu, an yi nadin mukamai a Rivers
An ce ana ci gaba da tantance waɗanda aka kama, kuma za a gurfanar da duk wanda aka samu da laifi a gaban kotu.

Asali: Getty Images
'Yan sanda za su cigaba da aiki a Abuja
Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da irin waɗannan samame lokaci zuwa lokaci domin kawar da barazana ga tsaron al’umma.
Ta kuma buƙaci goyon bayan jama’a wajen bayar da rahoton duk wani motsi ko mutum da ake zargi da hannu cikin laifuffuka, domin gudanar da aiki cikin nasara.
Rundunar ta nanata kudurinta na tabbatar da zaman lafiya da kariyar duk wani mai bin doka a fadin babban birnin tarayya.
An bukaci sauya fasalin aikin 'yan banga
A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar wakilai mai kula da kwamitin sojin kasa ya bukaci a sake nazari kan lamarin tsaron cikin gida a Najeriya.
'Dan majalisar ya yi magana ne bayan an zargi wasu 'yan banga da hannu a kisan Hausawa 16 da suka fito daga Fatakwal zuwa Kano a jihar Edo.
Ya kara da cewa dole a rika ba 'yan banga horo na musamman da saka ido kan ayyukan da suke gudanarwa a fadin Najeriya domin kaucewa samun matsala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng