‘Ku Bar Mani Jaje’: Ƴar Tsohon Gwamna da Ya Mutu Ta Barranta da Marigayin, Iyalansa
- Ƴar tsohon gwamnan jihar Oyo, Cif Omololu Olunloyo ta bayyana cewa ta fita daga cikin dangin Olunloyo baki daya
- Kemi Olunloyo ta ce ba za ta karbi gaisuwar mutuwar mahaifinta ba, saboda abubuwan da suka faru tsakaninsu da suka tarwatsa dangi gaba daya
- Kemi ta bayyana cewa mahaifinta ya cutar da su tun suna yara, ya kuma ruguza zaman lafiya da hadin kan iyalansu baki daya
- Ta kara da cewa mahaifinta ya shiga harkar tsafi, kuma hakan ya kara dagula zaman lafiyar su a cikin iyali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Ƴar marigayi tsohon gwamnan Oyo, Kemi Olunloyo ta bayyana cewa ta dena daukar sunan danginsu, Olunloyo, baki daya.
Ta kuma ce ba za ta karbi gaisuwar rasuwar mahaifinta ba, wanda ya rasu ranar Lahadi, 6 ga Afrilun 2025 yana da shekara 89.

Asali: Facebook
'Ban son jaje': Ƴar marigayi tsohon gwamnan Oyo
Kemi ta bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na Facebook a jiya Laraba 9 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar ta fadi wasu abubuwan da suka faru a cikin iyalinsu da suka jawo rabuwar kawuna da rushewar zaman lafiya a gidansu.
A cikin sanarwar da ta wallafa a Facebook, Kemi ta ce:
"Na saka bidiyo a TikTok kan mutuwar mahaifina, ba ni cikin dangin Olunloyo yanzu, ba zan karbi gaisuwar kowa ba, ku tafi ku aika gaisuwa a facebook.com/omololuolunloyo."
"Na yafewa mahaifina duk da abubuwan da ya yi min a rayuwarsa, ba ku san abin da ke faruwa a dangina ba, haka nan ni ma ban san naku ba."
"Mahaifina Victor Omololu Olunloyo mutum mai fuska biyu ne, daban ga duniya, daban ga iyalinsa, ya rusa zaman lafiyar mu."

Asali: Instagram
Zarge-zargen da ƴar tsohon gwamnan ta yi masa
Ta zargi mahaifinta, Chif Omololu Olunloyo da cewa ya azabtar da su ta fuskoki da dama wanda ya taba musu zuciya har da gangar jiki.
Ta ce:
"Ya azabtar da mu tun muna yara, ya cutar da mu ta fuskar jiki da ta zuciya, ya tarwatsa iyali.
"Mahaifina ya nuna kamar ni ce diyar da yafi so, amma wannan ba gaskiya bane, ya cutar da ni da iyayena."
Kemi ta zargi mahaifinta da cewa ya yi amfani da kyawawan halayyarta wajen moriyar kansa, kuma ya yi mata abubuwa da dama.
Ta ce mahaifin nata ya tsunduma sosai cikin harkar tsafi da aljannu, har ya bayyana hakan a ranar zagayowar haihuwarsa na 80.
Kemi ta bayyana cewa matsalolin cikin dangin Olunloyo sun fara ne lokacin da mahaifinsu ya auri Aderonke Omololu Olunloyo.
Tsohon gwamnan jihar Oyo ya rasu
Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Oyo, Dr. Omololu Olunloyo, ya yi bankwana da duniya da safiyar ranar Lahadi, 6 ga watan Afirilun 2025.
Marigayin wanda ya taɓa zama shugaban farko na Kwalejin Fasaha ta Ibadan ya rasu ne ƴan kwanaki kaɗan kafin cikarsa shekara 90 a ban kasa.
Kafin rasuwarsa ya riƙe muƙamai daban-daban ciki har da na sarautun Balogun na Oyo da Otun Bobasewa na Ife.
Asali: Legit.ng