Yan sanda sun gayyaci Kemi Olunloyo don amsa tambayoyi
1 - tsawon mintuna
Shin tayi wani abunda ya saba ma shari’a ne?
Yar jarida mai kawo rudani Kemi Omololu-Olunloyo ta sanar da hakan ne a shafinta na Instagram cewa maza a hukumar yan sandan Najeriya sun mamaye gidanta na Ibadan don daukarta zuwa amsa tambayoyi.
KU KARANTA KUMA: Shugaban APC zai gana shugaban kasa Buhari, da sauran su kan taron al’ada
Koda dai ba’a san dalilin kamun nata ba tukuna, ‘yar tsohon gwamnan Oyo tace an fada mata cewa ba dalilin laifi bane.
Kalli rubutun ta:
A watan Fabrairu, 2017, wata yar wasan Nollywood Georgina Onuoha ta je Ibadan don ta kama Kemi a wata yarjejeniya inda ‘yar gwamnan ta ki mika wuya.
Asali: Legit.ng