Najeriya Ta Ƙara Yin Rashi, Tsohon Kwamishina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Cif Maja Umeh, wanda ya kasance babban jigo a jam'iyyar APGA kuma tsohon kwamishina a jihar Anambra ya riga mu gidan gaskiya
- An rahoto cewa Umeh ya kamu da ciwon bugun jini a 2022 amma ya samu sauƙi a kwanakin baya har ya halarci zaɓen fidda gwani na APGA a Anambra
- Legit.ng ta ruwaito cewa Umeh ya rasu yana da shekara 64, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da ke Awka, a ranar Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Awka, jihar Anambra - Tsohon kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da yawon buɗe ido a Jihar Anambra a zamanin gwamnatin Peter Obi, Maja Umeh, ya riga mu gidan gaskiya.
Umeh, wanda babban jigo ne a jam'iyyar APGA mai mulki a jihar Anambra, ya rasu ne a ranar Laraba, 9 ga Afrilu, yana da shekaru 64 da haihuwa a duniya.

Kara karanta wannan
Mai magana da yawun PDP ya yi murabus daga muƙaminsa, ya tona asirin wasu shugabanni

Source: Twitter
Legit.ng ta tattaro cewa Cif Umeh ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu (COOUTH) da ke Amaku-Awka, babban birnin jihar Anambra.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon kwamishina ya rasu a Anambra
A cewar majiyoyi daga danginsa, jigon jam’iyyar APGA ya cika ne da misalin ƙarfe 3:20 na rana a sashen ba da kulawar gaggawa na asibitin.
Shugaban ƙungiyar al’ummar garin Amichi da ke ƙaramar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra, Cif Cletus Chibuzor Udebuani, garin da marigayin ya fito ya tabbatar da rasuwa.
Chibuzora ya tabbatar da rasuwar tsohon kwamishinan a wata tattaunawa ta wayar salula da wakilin Legit.ng.
Ya bayyana mutuwar Umeh a matsayin babban rashi ga al’ummar garin Amichi, jihar Anambra da Najeriya baki ɗaya.
Jam'iyyar APGA ta tabbatar da rasuwar Umeh
Shugaban jam’iyyar APGA na jihar Anambra, Cif Ifeatu Obi-Okoye, shi ma ya tabbatar da lamarin ga wakilin Legit.ng, sai dai ya ce jam’iyyar za ta fitar da sanarwa a hukumance nan gaba kaɗan.

Kara karanta wannan
APC na ragargazar 'yan adawa a Kano, Barau ya karbi shugabannin jam'iyyar hamayya
Wannan dai babban rashi ne ga jam'iyyar AGPA a daidai lokacin da take tunkarar zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda za a yi ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya kamu da rashin lafiya ta bugun jini a 2022 amma ya samu sauƙi har ya halarci zaɓen fidda ɗan takarar gwamna na APGA.
An ce Umeh ya rasu ne bayan wata rashin lafiya da ta kama shi wadda aka yi gaggawar kai shi abibiti amma rai ya yi halinsa a sashen ba da kulawa ta musamman.
Kakakin APC a Ogun ya kwanta dama
A wani labarin, kun ji cewa sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar APC reshen jihar Ogun, Alhaji Abdulraheem Tunde Oladunjoye ya kwanta dama bayan fama da jinya.
Iyalansa sun tabbatar da rasuwar a wata sanarwa, suna mai cewa nan ba da jimawa ba za su sanar da lokacin da za a masa jana'iza.
Gwamna Dago Abiodun na Ogun ya miƙa sakon ta'aziyyarsa, inda ya bayyana rasuwar tsohon kakakin APC a matsayin mai wahalar jure wa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng