Gaba da Gabanta: Umarnin da Kotu Ta ba Shugaban Riko a Rivers bayan Saba Mata
- Wata kotun tarayya da ke Port Harcourt ta bukaci shugaban riko a Rivers ya bayyana dalilin da yasa ba za a dakatar da nadin shugabannin riko na kananan hukumomi ba
- Wannan umarni ya biyo bayan karar da wata kungiya tare da shugabanta, Courage Nsirimovu suka shigar kan nadin shugabannin kananan hukumomi
- Lauyan masu karar, A. O. Imiete, ya roki kotu da ta amince da bukatunsu, yana mai cewa nadin na iya kawo cikas ga dimokuradiyya
- Mai shari’a Adamu Turaki Mohammed ya dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Afrilu, 2025, domin ci gaba da sauraren shaidu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Kotun tarayya da ke Port Harcourt ta umurci shugaban riko a jihar Ribas da ya bayyana a gabanta cikin gaggawa.
Kotun ta ba da umarnin ne bisa dalilin da yasa ba za a dakatar da nadin shugabannin kananan hukumomi ba.

Asali: Facebook
Matakin da kotu ta dauka kan Kantoman Rivers
Mai shari’a Adamu Turaki Mohammed ne ya bayar da wannan umarni ranar Litinin, 7 ga watan Afrilu, 2025, bayan karar da wata kungiya ta shigar, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu karar sun bukaci kotu da ta hana shugaban riko a jihar Rivers da mukarrabansa ci gaba da nadin shugabannin kananan hukumomi saboda yana iya dagula tsarin dimokuradiyya.
Mai shari’a Mohammed ya ce dole a yi adalci, don haka ya umurci wanda ake kara da ya bayyana dalilin da yasa ba za a hana nadin ba.
Kotun ta kuma fitar da takardar gayyata ga wanda ake kara sannan ta dage sauraren karar zuwa ranar 14 ga watan Afrilu, 2025.
Lauyan masu karar, A. O. Imiete, ya roki kotu da ta amince da bukatunsu, yana mai gabatar da rubutacciyar takardar hujja a gaban kotu.

Kara karanta wannan
Bayan Wike ya gana da 'yan majalisa, an bijirewa kotu, an yi nadin mukamai a Rivers
Wanda ake kara bai halarci kotun ba yayin zaman sauraren karar, lamarin da ya sa ake sa ran ci gaba da duba shari’ar a gaba.

Asali: Facebook
Musabbabin shigar da kara kan Ibok-Ete Ibas
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun zazzafar muhawara a jihar Rivers kan nadin shugabannin riko na kananan hukumomi da bin doka yadda ya kamata.
Masu lura da lamuran siyasa a jihar na jiran yadda wannan kara za ta kaya, kasancewar tana iya zama darasi ga sauran shugabanni a jihar.
An sanya lambar shari’ar a matsayin FHC/PH/CS/46/2025, kuma har yanzu al’umma na ci gaba da bibiyar yadda shari’ar za ta kare.
Shugaban riko a Rivers ya yi nade-nade
Kun ji cewa Shugaban riko a Rivers ya naɗa shugabannin riko a kananan hukumomi 23 na jihar duk da kotu ta hana.
Kotu a Port Harcourt ta hana Ibas ɗaukar irin wannan mataki, tana mai cewa ba shi da hurumin yin nadin bisa dokar kasa.
Ana ganin matakin da Ibas ya dauka zai iya kara hura wutar rikici a cikin rikicin siyasa da shari’a da ke ci gaba da kara zafi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng