2027: Kungiyoyin Arewa 65,000 Sun Bayyana Matsayarsu kan Takarar Tinubu

2027: Kungiyoyin Arewa 65,000 Sun Bayyana Matsayarsu kan Takarar Tinubu

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu tagomashi muddin zai nemi ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027
  • Ƙungiyar matasan Arewa (ACY) ta bayyana cewa ta shirya ba da cikakken goyon baya ga shugaban na Najeriya
  • Shugaban ƙungiyar Hon. Abubakar Aliyu ya bayyana cewa akwai dubunnan matasan Arewa da ke tare da Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Ƙungiyar matasan Arewa ta ACY ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ƙungiyar ta bayyana cewa sama da ƙungiyoyi 65,000 daga Arewa za su kaɗa ƙuri’a domin Bola Tinubu ya sake lashe zaɓe a 2027.

Bola Ahmed Tinubu
Kungiyoyin Arewa 65,000 za su zabi Tinubu a 2027 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ƙungiyoyin Arewa sun nuna goyon baya ga Tinubu

Darakta Janar na ƙungiyar, Hon. Abubakar Aliyu, wanda aka fi sani da Galadiman Takai, ya bayyana hakan lokacin da yake magana da manema labarai a Kaduna, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Ana batun hadaka, shugaba a APC ya fadi tagomashin da Arewa ta samu a mulkin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa goyon bayansu ga shugaban ƙasan ya samo asali ne saboda irin ayyukan da Tinubu ya gudanar cikin shekararsa ta farko a mulki.

“Mun shirya wannan taron manema labaran ne domin mu bayyana cikakken goyon bayanmu ga mai girma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu."
"A matsayinmu na ƴan Najeriya, mun sha ganin gwamnatoci daban-daban, amma abin da muke gani a ƙarƙashin Shugaba Tinubu abin mamaki ne."

- Hon. Abubakar Aliyu

An jero nasarorin gwamnatin Bola Tinubu

Galadiman Takai ya bayyana wasu daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu, ciki har da ayyuka a faɗin ƙasar nan kamar samar da gas na CNG, da kuma nasarori wajen jawo masu zuba hannun jari na cikin gida da na waje.

"Ƙungiyar ACY tana da mambobi sama da miliyan biyu da ke da katin zaɓe (PVC), kuma za su fito kwansu da kwarkwatarsu domin kaɗa ƙuri’a ga Shugaba Tinubu a 2027."

Kara karanta wannan

Ndume ya tono fada kan sukar Tinubu, fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi

"Muna da yakinin cewa da haɗin kai, za mu samar da makoma mai kyau ga ƙasarmu."

- Hon. Abubakar Aliyu

Bola Ahmed Tinubu
Tinubu ya samu goyon baya a Arewa Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙi, tsaro, da walwalar jama’a musamman a yankin Arewa.

“Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne, maza da mata da dama ƴan Arewa sun samu manyan muƙamai a gwamnati, kamar sakataren gwamnatin tarayya, ministan tsaro, ministan harkokin jin ƙai da sauransu."

- Hon. Abubakar Aliyu

Ƙungiyar ta kuma jaddada ƙudirinta na ci gaba da nuna goyon baya ga haɗin kai da ci gaban ƙasa, tare da kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da marawa Shugaba Tinubu baya.

Tinubu ya samu yabo a Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a yankin Arewa maso Yamma, Garba Datti Mohammed, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Babban basaraken Igbo ya gargadi 'yan Arewa kan kisan mafarauta a Edo? An ji gaskiya

Jagoran na APC ya yabi shugaban ƙasan ne kan yadda ya ba da muƙamai masu gwaɓi ga ƴan Arewa a gwamnatinsa.

Ya bayyana cewa abin da shugaban ƙasan ya yi, ba a taɓa ganin irinsa ba a gwamnatocin da suka gabata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel