"Daga Gadon Asibiti na Taso": EFCC Ta Taso Ministan Buhari, Ta Kunna Bidiyonsa a Kotu

"Daga Gadon Asibiti na Taso": EFCC Ta Taso Ministan Buhari, Ta Kunna Bidiyonsa a Kotu

  • EFCC ta kunna bidiyon da ta ɗauka yayin yi wa tsohon ministan makamashi, Saleh Mamman tambayoyi kan badakalar aikin Mambila a kotu
  • A faifan bidiyon, an ji tsohon ministan na faɗawa jami'an EFCC cewa ba shi da lafiya domin daga gadon asibiti ya taso don ya amsa gayyatarsu
  • Lauyan EFCC ya shaidawa alkalin kotun tarayya mai zama a Abuja cewa sun nuna bidiyon ne domin tabbatar da ingancin shaidar da za su gabatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Ministan Makamashi, Saleh Mamman, ya bayyana cewa daga gadon asibiti ya taso domin amsa gayyatar jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC)

Saleh Mamman, wanda ya riƙe muƙamin minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari na fuskantar tuhume-tuhumen almundahana a EFCC.

Tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman.
EFCC ta kunna bidiyon tsohon ministan makamashi a gaban kotu Hoto: Saleh Mamman
Asali: Facebook

Rahoton Leadership ya nuna cewa tsohon minista ya ce haka nan ya hakura ya taso daga gadon asibiti domin amsa gayyatar jami'an EFCC.

Kara karanta wannan

"Mutum 1 ke juya APC," Tsohon mataimakin shugaban PDP ya faɗi shirin da suke yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta nuna bidiyon Saleh Mamman

Ya bayyana hakan ne awani faifan bidiyo da aka nuna a kotu yayin zaman shari'a kan tuhume-tuhumen da EFCC take masa na karkatar da kuɗin al'umma.

Saleh Mamman ya shaida wa Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja cewa ya sha sanar da EFCC cewa ba ya cikin koshin lafiya.

Tun farko, lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), ya ce dalilin gabatar da faifan bidiyon shi ne domin tabbatar da cewa shaidar da hukumar za ta gabatar ta

Amma Lauyan ministan, Femi Atte (SAN), ya musanta hakan inda ya ce an tilasta wa Saleh Mamman yin bayanai a lokacin da ba ya cikin hayyacinsa, kuma ya sha fada musu cewa daga gadon asibiti yake.

EFCC ta taso tsohon minista daga gadon asibiti

A cikin bidiyon, Mamman ya bayyana cewa daga gadon asibiti ya fito domin girmama gayyatar EFCC.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: Hedkwatar tsaro ta fito da bayanin yadda aka ceto Janar Tsiga

Har ila yau, ya musanta mallakar wani gida da ke unguwar Wuse 2 a Abuja lokacin da jami’an EFCC suka tambaye shi.

An nuna bidiyon wanda tsawonsa ya kai sa’o’i biyu da mintuna 39 a kotu. Mamman yana amsa tambayoyin a harshen Hausa, yayin da mai fassara na kotu ke fassarawa zuwa Turanci.

A wasu lokuta, mai fassarar na ce wa alkalin kotu: “Mai shari’a, ban fahimta da kyau ba. Zan wuce inda ban fahimta ba.”

Alkalin kotun ya amsa da cewa: “Fassara abin da ka ji.”

Saleh Mamman.
Saleh Mamman ya ce daga asibiti ya wuce ofishin EFCC domin mutunta gayyatar da aka masa Hoto: Saleh Mamman, EFCC
Asali: Facebook

Minista ba shi da ikon cire kudi a asusun aikin

A zaman kotun da ya gabata ranar 19 ga Maris, ma’aikaciyar Babban Bankin Najeriya (CBN), kuma shaidar EFCC ta 15 , ta ce CBN ne ke kula da asusun aikin wutar Manbila a madadin Ofishin Akanta Janar na Ƙasa (OAGF).

Okoroafor Chinyere, mataimakiyar manaja a sashen biyan kudade na cikin gida a CBN, ta faɗi haka yayin amsa tambayoyi daga Lauyan wanda ake kara, Mr. Atte.

Kara karanta wannan

'Ana kulla wa Ribas makirci,' Kwamishinan Fubara ya hango sabuwar matsala

Ta tabbatar wa kotu cewa EFCC ta aika wa CBN da wasiƙa tana neman bayanai kan ma’aikatar wutar lantarki, kuma sun ba da bayanan.

Yayin bayani kan asusun aikin (wanda aka gabatar da takardunsa a matsayin shaida), Okoroafor ta ce CBN ke kula da asusun a madadin OAGF.

Lokacin da aka tambaye ta ko minista ko ofishinsa na da ikon bada izinin cire kudi daga asusun, ta ce: “Ba zan iya cewa komai ba.”

EFCC ta gurfanar da Akanta Janar

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta gurfanar da Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja kan zargin karkatar da biliyoyin kudi.

EFCC ta gurfanar da Akanta Janar ɗin tare da wani ɗan canji mai suna Aliyu Abubakar da kamfaninsa a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

An gurfanar da su ne bisa tuhume-tuhume tara da suka shafi halasta kuɗin haram da sama da faɗi da dukiyar al'umma a Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel