Ana Batun Hadaka, Shugaba a APC Ya Lissafo Tagomashin da Arewa Ta Samu a Mulkin Tinubu
- Mataimakin shugaban APC na ƙasa a yankin Arewa maso Yamma, Garba Datti Mohammed ya yi magana kan salon mulkin Bola Tinubu
- Garba Datti Mohammed ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu yana damawa da Arewa a gwamnatinsa, akasin tunanin wasu 'yan yankin
- Tsohon 'dan majalisar na Sabon Gari a jihar Kaduna ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya ba da muƙami masu gwaɓi ga bangaren Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa (yankin Arewa maso Yamma), Garba Datti Muhammad, ya kare gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Garba Datti Muhammad ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana yin aiki tuƙuru wajen inganta ci gaban Arewa da jin daɗin al’ummarta.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta rahoto cewa mataimakin shugaban na APC ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Garba Datti wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne, ya kuma buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, da su yi taka tsan-tsan kan zaɓen 2027.
Ya ce ya kamata tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya haƙura da sake shiga takarar shugaban ƙasa sannan ya riƙe mutuncinsa a matsayin dattijon ƙasa.
Jagora a APC ya ce Tinubu na damawa da Arewa
A cewarsa, yankin Arewa maso Yamma ya samu ayyukan ci gaba a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Ya ce yankin bai taɓa lokacin da ake damawa da shi ba a cikin gwamnati kamar a wannan karon da Tinubu yake shugaban ƙasa.
Ya ce yankin Arewa ya samu muƙamin shugaban majalisar wakilai daga jihar Kaduna da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa daga jihar Kano.

Asali: Facebook
Wane tagomashi yankin Arewa ya samu?
"Ba a taɓa samun wani lokaci a tarihin Najeriya inda shugabannin majalisar tarayya biyu suka fito daga yanki ɗaya ba. Haka kuma, muna kuma da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa daga jihar Kano."
"Baya ga haka, yankin Arewa maso Yamma ya samu muƙamai 12 na ministoci, ciki har da waɗanda ke jagorantar manyan ma’aikatu kamar ministocin tsaro guda biyu, kasafin kuɗi da muhalli."
"Ministocin gidaje guda biyu, al’adu da tattalin arzikin fikira, ƙananan ministocin babban birnin tarayya Abuja, ilmi, ayyuka da sauransu."
"Yankin Arewa kuma yana da hafsoshin tsaro guda biyu, babban hafsan tsaron ƙasa daga jihar Kaduna, hafsan sojojin sama daga jihar Kano."
"Gwamnatin Tinubu kuma tana aiki tuƙuru domin inganta rayuwar ƴan Najeriya bayan cire tallafin man fetur. Darajar Naira tana ƙara ƙarfi a kullum. Farashin kayan abinci na raguwa sosai. Tattalin arziƙi na farfaɗowa a hankali."
An caccaki Ndume saboda sukar Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta yi wa Sanata Ali Ndume martani kan sukar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce akwai munafurci a irin sukar da Sanata Ndume yake yi wa Tinubu.
Ya buƙaci sanatan na Borno da Kudu da ya riƙa yin suka mai ma'ana maimakon ya riƙa yaɗa bayanan da babu ƙamshin gaskiya a cikinsu.
Asali: Legit.ng