Alkali Ya Sha da Kyar bayan Yan Ta'adda Sun Yi Ram da Shi a Katsina
- Dakarun soji sun kai daukin gaggawa a kauyen Mahuta, Dandume, jihar Katsina a daren Litinin, 8 ga Afrilu, 2025 bayan yan ta'adda sun fatattaki garin
- Yan bindigar sun yi garkuwa da mutum shida, ciki har da Rabiu Tukur, alkali a Kotun Shari’a ta ƙasa da ke Dandume kuma sun fara shirin tafiya da su
- Sojoji sun kai agajin gaggawa, lamarin da ya jawo wani artabu a tsakaninsu da 'yan bindiga dauke da miyagun makamai bayan sun sace jama'a
- Daga karshe, an yi nasarar ceto Mai shari'a Rabiu Tukur, sai dai har yanzu ba a san makomar sauran mutum biyar da aka sace su tare ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina –Sojojin Najeriya sun dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai a kauyen Mahuta da ke karamar hukumar Dandume, jihar Katsina, a daren Litinin, 8 ga Afrilu, 2025.
A yayin harin, an sace mutane shida, ciki har da wani alkali da ake girmama wa a yankin, Malam Rabiu Tukur mai shekara 49, wanda ke aiki a Kotun Shari’a ta ƙasa da ke Dandume.

Asali: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa, harin ya faru da misalin 11:55 na dare, lokacin da wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka mamaye kauyen suka yi awon gaba da wasu mazauna unguwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda aka sace har da Alkali Tukur, wanda mutane da dama ke ganin mutuncinsa, musamman ganin irin aikin da ya ke yi a yankin.
Jam’an tsaro sun kai dauki a kauyen Katsina
Bayan harin, majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar da cewa sojoji sun kai masu agajin gaggawa, inda suka gwabza artabu da ‘yan bindiga.
A yayin wannan gwabza wa ne sojojin suka samu nasarar kubutar da Malam Tukur ba tare da ya samu wani rauni ba.

Asali: Twitter
Ko da yake an ceto Alkali Tukur lafiya, amma har yanzu ana ci gaba da kokarin gano inda sauran mutum biyar da aka sace suke.
Ana neman mutanen Katsina da aka sace
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kara zafafa bincike da aikin ceto a yankunan da ke kewaye da Mahuta domin gano inda suka shiga da kubutar da su.
Wannan lamari ya sake haska matsalolin tsaro da ke addabar al’ummomi a Arewacin Najeriya, inda hare-haren ‘yan bindiga ke kara barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a.
Hukuma na kira ga jama’a da su kasance cikin shiri da kuma hada kai da jami’an tsaro don tabbatar da tsaro da aminci a yankunansu.
'Yan bindiga sun sace malami a Kaduna
A baya, mun wallafa cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani babban malamin addinin Kirista a safiyar Talata, 8 ga Afrilu, 2025.
Lamarin ya faru ne a Mararaba Abro, a karamar hukumar Sanga, inda 'yan ta’addar suka kai farmaki gidan Fasto Samson Ndah Ali, malamin Cocin ECWA, suka kuma yi awon gaba da shi.
Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigar dauke sun kutsa cikin gidan ne da misalin karfe 12:45 na dare, inda suka yi amfani da karfi suka fitar da malamin daga cikin iyalansa.
Asali: Legit.ng