Abin da Muka Sani game da Jita Jitar Mutuwar Sheikh Junaidu Abubakar Bauchi

Abin da Muka Sani game da Jita Jitar Mutuwar Sheikh Junaidu Abubakar Bauchi

  • Imam Junaidu Abubakar Bauchi ya bayyana cewa yana raye kuma cikin koshin lafiya, ya karyata jita-jitar da ake yadawa game da mutuwarsa
  • Babban malamin ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yana jaddada cewa labarin ba gaskiya ba ne
  • Malamin ya bayyana yadda ya samu kiraye-kiraye daga 'yan uwa da abokai suna jajanta masa, amma ya tabbatar musu cewa yana cikin koshin lafiya
  • Sheikh Junaidu ya yi addu'a yana rokon Allah ya ba su ikon tuba kafin mutuwa tare da shawartar jama'a su nemi yardar Ubangiji a rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Babban malamin Musulunci, Imam Junaidu Abubakar Bauchi ya yi martani kan jita-jitar mutuwarsa da ake yaɗawa.

Malamin musuluncin ya ƙaryata rade-radin da ake yaɗawa a kafofin sadarwa cewa ya riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

'Ba ni ba neman sanata': Gwamna ya ce yana gama wa'adinsa zai yi ritaya a siyasa

Sheikh Junaidu ya yi martani kan labarin mutuwarsa
Sheikh Imam Abubakar Bauchi ya ce yana nan cikin koshin lafiya. Hoto: Imam Junaidu Abubakar Bauchi.
Asali: Facebook

Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Talata 8 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yada mutuwar Imam Junaidu

Hakan ya biyo bayan yada jita-jita kan cewa Allah ya karbi rayuwar malamin a ranar Litinin 7 ga watan Afrilun 2025.

Mutane da dama sun yi Allah wadai ya jita-jitar inda suke cewa idan lokacin mutuwar mutum ya yi babu mai hanawa.

Martanin da Imam Junaidu Bauchi ya yi

A cikin faifan bidiyon, malamin ya ce yana cikin koshin lafiya ba kamar yadda ake fada ba.

Sanarwar ta ce:

"Yan uwa Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barka tuhu, a yau na samu kiranye-kiranye daga ƴan uwa da abokan arziki.
"Suna alhini suna jajantawa wai sun ji wani labari a kaina, lallai wannan labari ba gaskiya ba ne.
"Muna nan muna cikin taimakon Manzon Allah, muna cikin albarkar Manzon Allah."

Kara karanta wannan

'Abin da Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya faɗa kafin rasuwarsa': Ɗalibinsa ya magantu

Imam Junaidu ya yi martani kan jita-jitar mutuwarsa da ake yaɗawa
Imam Junaidu Abubakar Bauchi ya shawarci al'umma bayan yada labarin mutuwarsa. Hoto: Imam Junaidu Abubakar Bauchi.
Asali: Facebook

Addu'ar da Imam Junaidu ya yi

Malamin ya yi addu'a inda ya roki Allah ya ci gaba da barinsu a taimakon Manzon Allah da kuma neman albarkar Manzon Allah.

Malamin ya kara da cewa:

"Muna rokon Allah ya tabbatar da mu a kan hanya madaidaiciya kuma ya sa farkonmu ya fi ƙarshenmu kyau.
"Muna rokon Allah ya ba mu ikon tuba kafin mutuwa, ya hore mana wadanda za su yi mana addu'a bayan ba mu nan."

Ya shawarci al'umma su mayar da hankali wurin neman yardar Allah saboda wanda yake raye shi ne ke da aiki a gabansa fiye da wanda ya mutu.

Malamin Musulunci ya rasu a Kebbi

Mun ba ku labarin cewa Allah ya karbi rayuwar Sheikh Imam Bello Jandutsi, wanda shi ne limamin masallacin Sheikh Abbas Jega da ke jihar Kebbi.

Marigayin ya kwashe fiye da shekaru 30 yana limanci da koyar da addinin Musulunci a cikin masallacin Juma’a na Sheikh Abbas Jega da ke Birnin Kebbi.

A wata sanarwa da kungiyar Izala ta fitar ta nuna cewa an yi sallar jana’izar malamin a ranar Talata 8 ga watan Afrilun 2025 da karfe 10:00 na safiya, a masallacin Sheikh Abbas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel