Ndume Ya Tono Fada kan Sukar Tinubu, Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Martani Mai Zafi
- Fadar shugaban ƙasa ba ta ji daɗin sukar da Sanata Ali Muhammad Ndume ya yi wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba
- Mai magana da yawun bakin Tinubu ya yi wa Ndume kaca-kaca kan zargin nuna bambanci a naɗe-naɗen da shugaban ƙasan yake yi
- Bayo Onanuga ya buƙaci Sanatan na Kudancin Borno da ya daina yaɗa bayanan ƙarya sannan ya riƙa yin suka mai ma'ana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta yi wa Sanata Ali Ndume martani kan zargin nuna bambamci a naɗe-naɗen muƙamai da Bola Tinubu ke yi.
Fadar shugaban ƙasan ta ƙaryata zargin da Ndume ya yi, inda ta bayyana iƙirarin da sanatan ya yi a matsayin nuna son kai da yaudara.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ga fitar a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Gwamna Uba Sani ya dauko hanyar faranta ran ma'aikatan da suka yi ritaya a Kaduna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fadar shugaban ƙasa ta caccaki Ali Ndume
Bayo Onanuga ya bayyana cewa Sanata Ali Ndume mutum ne mara son gaskiya kuma mai son jawo rigima.
Martanin na Onanuga ya biyo bayan zargin da Sanata Ndume ya yi cewa Shugaba Tinubu na fifita wasu yankuna a naɗe-naɗen da ya ke yi, wanda hakan a cewarsa ya saɓawa kundin tsarin mulki.
“Maganganun da Sanata Ali Ndume ya yi a kafar talabijin dangane da abin da ya kira naɗe-naɗen da ba su da adalci daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, cike suke da munafurci."
“Yayin da sanatan na Borno ke neman bayyana kansa a matsayin gwarzon adalci, ya manta ya faɗawa wanda ke tambayarsa cewa mutane biyu daga yankinsa sun samu manyan muƙamai a sababbin naɗe-naɗen da aka yi a kamfanin NNPCL."
“Idan zaɓin Tinubu da wakilansa na nuna ƙabilanci ne, to ta yaya mutane biyu daga yankin Ndume suka samu manyan muƙamai a NNPCL?"
- Bayo Onanuga
Hadimin shugaban ƙasan ya zargi Ndume da yin yawan magana marar tushe da nufin farantawa jama’a rai ba tare da dogaro da gaskiya ba.
“Halayensa na yawan sukar gwamnati ba tare da cikakken bayani ba, kuma daga baya a ƙaryata su da gaskiya, na nuna cewa ya fi son ɗaukar hankali da tada husuma fiye da yin suka mai ma'ana."
- Bayo Onanuga

Asali: Facebook
Fadar shugaban kasa ta kare Tinubu
Onanuga ya sake jaddada cewa Shugaba Tinubu na da kishin kafa gwamnati wadda za ta tafi da kowa, yana mai cewa naɗe-naɗen da ake yi sun dogara ne kan cancanta, gaskiya da wakilci daga dukkanin yankunan ƙasar nan.
Ya ce Shugaba Tinubu ya ƙudiri aniyar kafa gwamnati da ke rungumar ƴan Najeriya gaba ɗaya ba tare da la’akari da ƙabilanci ko yanki ba.
Ya buƙaci Ndume da ya gujewa yaɗa bayanan ƙarya da yin sukar da ba ta da tushe, yana mai gargadin cewa irin wannan hali na cutar da ƙasa kuma ba shi ne ake sa ran gani daga wajen sanatan Najeriya ba.
Sanatan APC ya caccaki Ali Ndume
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Sunday Karimi, ya caccaki takwaransa Ali Ndume.
Sunday Karimi ya taso Ali Ndume a gaba ne bayan ya soki gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Sanatan ya buƙaci Ndume da ya maida hankali wajen ganin an magance Boko Haram a yankinsa maimakon sukar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng