Gwamna Zulum Ya Tsage Gaskiya, Ya Fadi Fargabarsa kan 'Yan Boko Haram
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwa kan yawaitar hare-haren Boko Haram da ake samu
- Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa jihar Borno na fuskantar haɗarin sake komawa cikin rikici
- Gwamnan ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin ganin an murƙushe ƴan ta'adda a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi magana kan ƙaruwar hare-haren ƴan ta'addan Boko Haram.
Gwamna Zulum ya bayyana damuwa kan hare-haren da ƴan Boko Haram da suka kai a manyan sansanonin sojoji kwanan nan, yana mai cewa jihar na cikin haɗarin komawa cikin rikici.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar wani taron kwamitin tsaro da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Maiduguri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zulum ya koka kan hare-haren Boko Haram
Gwamna Zulum ya nuna damuwa kan yadda ƴan Boko Haram ke farmakar sansanonin sojoji a jihar.
“An tarwatsa sansanonin sojoji da dama, musamman a Wulgo, Sabongari, Wajirko da sauransu."
"Alamu na nuna cewa muna samun koma baya, kuma wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da ya kamata mu tattauna a kai."
"Zaman lafiya ya fara dawowa a Borno a hankali cikin shekaru uku da suka wuce, amma yanzu muna fuskantar hare-haren bazata lokaci zuwa lokaci."
- Gwamna Babagana Zulum
Zulum ya ba gwamnatin tarayya shawara
Ya buƙaci a tura jiragen yaƙi masu saukar ungulu da sababbin jiragen sintiri marasa matuƙa da aka sayo domin tallafawa ayyukan sojoji a wuraren da abin ya shafa.
Zulum ya ce an kira taron ne domin jin gaskiya daga manyan masu ruwa da tsaki ciki har da sarakunan gargajiya da shugabannin hukumomin tsaro na jihar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
“Yayin da muke yabawa rundunar sojojin Najeriya, ƴan sanda, DSS da kuma hukumomin tsaro na gwamnati wajen tabbatar da doka da oda a jihar, dole ne mu fadi gaskiya, domin idan ba haka ba, duk ci gaban da muka samu zai zama kamar tatsuniya ne."
- Gwamna Babagana Zulum

Asali: Facebook
Gwamnan, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas, ya roƙi gwamnatin tarayya da ta tabbatar yankin na samun kulawa ta musamman.
"Alamu na nuna cewa rundunar sojojin Najeriya da ma’aikatar tsaron tarayya ba su mayar da hankali sosai a kan jihohin Arewa maso Gabas ba."
"Idan aka yi la’akari da muhimmancin da wannan yanki ke da shi, muna da haƙƙin samun kulawar da ta dace."
- Gwamna Babagana Zulum
Sojoji sun gwabza da ƴan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi artabu da ƴsn ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
Sojoji sun yi fafatawar ne bayan ƴan ta'adɗan Boko Haram sun kai musu farmaki a sansaninsu da ke ƙaramar hukumar Gwoza.
A yayin artabun an hallaka sojoji guda biyu, ya yin da jami'an tsaro suka samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram masu yawa.
Asali: Legit.ng