Sanatan APC Ya Caccaki Ndume kan Sukar Gwamnatin Shugaba Tinubu

Sanatan APC Ya Caccaki Ndume kan Sukar Gwamnatin Shugaba Tinubu

  • Sanata Sunday Karimi bai ji daɗin kalaman da Ali Ndume ya yi ba dangane da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Sunday Karimi wanda ke wakiltar Kogi ta Yamma ya caccaki Sanata Ndume kan sukar gwamnatin Bola Tinubu da ya yi
  • Sanatan ya nuna cewa maimakon sukar gwamnati, kamata ya yi Ndume ya koma ya magance matsalar Boko Haram a mazaɓarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata Sunday Karimi (mai wakiltar Kogi ta Yamma) a ranar Talata ya caccaki Sanata Ali Ndume (mai wakiltar Borno ta Kudu).

Sanata Karimi ya caccaki Ndume ne kan kalaman da ya yi game da Bola Tinubu da kuma waɗanda ya kira karnukan farautar shugaban ƙasa.

Sunday Karimi ya caccaki Ndume
Sanata Sunday Karimi ya caccaki Sanata Ali Ndume Hoto: Senator Mohammed Ali Ndume, Sunday Karimi
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ambato Sanata Sunday Karimi na cewa ba sukar gwamnati ya kamata Ndume ya riƙa yi ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya aiko sako daga Faransa kan mutuwar shugaban MTN na farko

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ali Ndume ya caccaki gwamnatin Tinubu

Sanata Ndume dai ya soki abin da ya kira rashin bin doka da kuma yawan wuce gona da iri da gwamnati ke yi fiye da ƙima ƙarƙashin shugabancin Tinubu.

Ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta kauce hanya inda take gudanar da kasafin kuɗi guda uku lokaci guda sannan gwamnati na ciwo bashi ba tare da amincewar majalisar dokoki ta tarayya ba.

Haka kuma, ya ce gwamnati na watsi da batun tsaro duk da yawan kashe-kashe da ake yi a jihar Plateau, bayan abubuwan da suka faru a Edo, da kuma ƙaruwar hare-haren Boko Haram da ISWAP a jiharsa ta Borno.

Sanata Sunday Karimi ya caccaki Ndume

A martanin da ya yi, Sanata Karimi wanda shi ma mamba ne na jam’iyyar APC mai mulki kamar Ndume, ya caccaki sanatan na Borno ta Kudu.

Sanata Sunday Karimi ya ce maimakon Ndume ya riƙa fitowa fili yana sukar gwamnati, kamata ya yi matsayinsa na jagoran mutanensa, ya koma gida ya haɗa kai da su wajen magance matsalar Boko Haram.

Kara karanta wannan

Nada mukamai: Sanata Ndume ya dura kan Tinubu, ya ce bai tsoron me zai biyo baya

Ya bayyana cewa ƙasar nan ta yi asarar ɗimbin sojoji da tiriliyan-tiriliyan na Naira wajen yaƙar ƴan ta’adda a mazaɓar Sanata Ndume cikin shekaru 10 da suka gabata.

Sunday Karimi
Sunday Karimi ya yi wa Ali Ndume martani Hoto: Sunday Karimi
Asali: Facebook
"Maganar gaskiya, na rasa ɗaya daga cikin matasan jami’ai, wani kyaftin a rundunar sojoji daga mazaɓata, wanda ke aiki a yankin Ndume, makonni uku da suka wuce."
“Matasa da dama ƴan Najeriya sun rasa rayukansu suna kare mutuncin ƙasar nan."
“Fiye da kashi 50 cikin 100 na kudaden shiga na Najeriya a ƴan shekarun nan an kashe su wajen yaƙar ƴan ta’adda."
“Saboda haka, maimakon fitowa yana sukar gwamnati, ya kamata Sanata Ndume ya koma gida a matsayinsa na shugaba ya haɗa kai da mutanensa wajen magance matsalar Boko Haram."

- Sanata Sunday Karimi

Tinubu ya fusata kan kashe-kashe

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhininsa kan kisan da ƴan bindiga suka yi wa mutane a jihar Plateau.

Kara karanta wannan

'A tabbatar da adalci duniya ta gani,' Abba Gida Gida kan kisan Uromi'

Shugaban ƙasan ya baƴyana cewa gwamnatinsa ba za ta amince da kashe-kashen mutane ba gaira ba dalili ba.

Mai girma Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta zaƙulo waɗanda suka kai harin domin su fuskanci hukunci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng