Ana Rade Radin Tinubu Ya Tsige Shi, Mahmud Yakubu Ya Saka Labule da Ma'aikatan INEC

Ana Rade Radin Tinubu Ya Tsige Shi, Mahmud Yakubu Ya Saka Labule da Ma'aikatan INEC

  • Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya jagoranci taron mako-mako ana jita-jitar cewa an tsige shi, lamarin da ya janyo cece-kuce sosai
  • A cewar INEC, saƙon WhatsApp da ke cewa an sauke Yakubu kuma an nada Farfesa Bashiru Olamilekan ba shi da tushe, kuma karya ne tsagwaronta
  • A taron, kwamishinoni da dama sun halarta, ciki har da Olumekun da Agbamuche-Mbu, inda aka ce za a yanke matakai masu nasaba da zaɓe

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban hukumar zaɓe ta kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, yana jagorantar taron mako-mako na hukumar, kasa da awanni 24 bayan jita-jitar tsige shi ta yadu.

A ranar Litinin, wani saƙo da ya karade WhatsApp ya yi zargin karya cewa Shugaba Bola Tinubu ya tsige Yakubu daga mukaminsa.

INEC ta yi magana kan taron da Farfesa Mahmud Yakubu ke jagoranta a hedikwatar hukumar
Farfesa Yakubu Mahmud ya jagoranci taron shugabannin hukumar INEC a Abuja. Hoto:@inecnigeria
Asali: Facebook

An karyara jita-jitar tsige shugaban INEC

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan daliban jami'a a Kebbi cikin dare

A cikin sakon, an kuma ce shugaban kasar ya maye gurbin Mahmud Yakubu da Farfesa Bashiru Olamilekan, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta rahoto cewa wannan saƙo da bai da wani tushe ko madogara ya haifar da rudani a kafafen sada zumunta tun daga lokacin da ya fara yaduwa.

Mai magana da yawun shugaban hukumar INEC, Rotimi Oyekanmi, ya karyata jita-jitar tare da rokon al'umma da su yi wa Allah su yi watsi da ita, yana mai cewa "ba gaskiya ba ce.”

Ana sa ran Farfesa Yakubu, wanda wa'adinsa na biyu a INEC ke dab da karewa, zai kammala wa'adinsa a ƙarshen wannan shekara ta 2025.

Farfesa Yakubu ya jagoranci taron INEC

A ranar Talata, INEC ta wallafa a shafinta na X cewa an fara taron mako-mako na hukumar, inda shugaban hukumar, Yakubu yake jagorantar zaman a hedkwatarta da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Dalilin da zai sa Mahmud Yakubu ya bar shugabancin INEC a 2025 da wasu bayanai

Wasu daga cikin kwamishinonin da suka halarci taron sun haɗa da: Mista Sam Olumekun, Hajiya May Agbamuche-Mbu, Mista Kenneth Ukeagu, Farfesa Abdullahi Abdu Zuru da Dakta Baba Bila.

Sauran sun haɗa da: Malam Mohammed Haruna, Farfesa Kunle Ajayi, Farfesa Sani Adam (SAN), da sakataren hukumar, Hajiya Rose Orianran-Antony.

Abin da sanarwar hukumar INEC ta ce

Sanarwar INEC ta nuna cewa mahukuntan hukumar za su yanke muhimman matakai a wannan taro na ranar Talata.

Sanarwar INEC ta ce:

"An fara taron mako-mako na hukumar zaɓe ta kasa (INEC) a safiyar Talata a hedkwatar hukumar da ke Abuja, wanda shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ke jagoranta.
"Daga cikin kwamishinonin ƙasa da suka halarci taron akwai: Mista Sam Olumekun mni, Hajiya May Agbamuche-Mbu, Mista Kenneth Ukeagu, Farfesa Abdullahi Abdu Zuru, da Dakta Baba Bila.
"Sauran su ne: Malam Mohammed Haruna, Farfesa Kunle Ajayi, Farfesa Sani Adam (SAN), da Sakatariyar hukumar, Hajiya Rose Orianran-Anthony.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi maganar batun tsige shugaban INEC, Mahmud Yakubu

"Ana sa ran za a ɗauki muhimman matakai a wannan taro."

INEC: Gwamnati ta magantu kan sauke Mahmud

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin sadarwa, Daniel Bwala, ya musanta jita-jitar cewa Bola Tinubu ya tsige shugaban hukumar INEC.

Bwala ya tabbatar da cewa har yanzu Farfesa Mahmood Yakubu ne a kan kujerar shugaban hukumar INEC, domin babu wani sauyi da aka yi.

A cewar wata sanarwa da ya fitar, Bwala ya bayyana rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu shafukan intanet a matsayin ƙarya 'tsagwaronta.'

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng