Olubadan Ya Gargadi Fitaccen Sarkin Hausawa na Sasa kan Ikirarin Iko a Yankin

Olubadan Ya Gargadi Fitaccen Sarkin Hausawa na Sasa kan Ikirarin Iko a Yankin

  • Mai Martaba, Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya bayyana matsayin Sarkin Sasa a jihar Oyo bayan karɓar ragamar mulki
  • Olubadan ya bayyana haka ne yayin taron majalisar kwamitin Olubadan a fadarsa da ke Oke Aremo, Ibadan, babban birnin jihar Oyo
  • Basaraken ya bayyana cewa Chif Akinade Ajani Amusa shi ne Baale na Sasa, kuma wakilin hukuma na masarautar Ibadan a yankin Sasa
  • Ya gargadi mutane da su mutunta Baale na Sasa, yana mai cewa duk wanda ya saba haka zai fuskanci hukunci mai tsanani

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Sarkin Ibadan da ake kira, Olubadan, Owolabi Olakulehin, ya bayyana matsayin Sarkin Sasa a Jihar Oyo.

Basaraken ya ce doka ba ta san da shi ba a matsayin wakilin Olubadan ba inda ya ce ba shi da inganci.

Kara karanta wannan

'Babu hannun kowa a naɗinsa': Gwamna kan naɗa fitaccen Sarki mai daraja ta 1

An gargadi Sarkin Hausawa a Kudu kan nadinsa
Olubadan a jihar Oyo ya sha alwashin daukar mataki kan naɗinsa ba bisa doka ba. Hoto: Alh. Kaseem A Yaro.
Asali: Facebook

Olubadan ya bayyana hakan ne a jiya Litinin 8 ga watan Afrilun 2025 yayin taron majalisar Olubadan da aka gudanar a fadarsa, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi rashin Sarkin Sasa a Oyo

Marigayi Alhaji Haruna Maiyasin Katsina ne ya rike wannan mukami, kuma shi ne shugaban majalisar sarakunan Arewa a jihohin Kudu goma 17.

Allah ya yi karbi rayuwar basaraken a jihar Oyo bayan ya shafe shekaru da dama kan karagar mulki musamman na Hausawa a yankin.

An yi sallar jana'izarsa a ranar Lahadi 2 ga watan Maris din shekarar 2025 yayin da Sarakunan Hausawa da malaman addini suka yi alhinin rashinsa fadarsa.

Nadin magajin marigayi Sarkin Sasa

An nada dansa, Ahmed Haruna (Ciroma) wanda iyalinsa da sarakunan Arewa na Kudu suka amince da shi matsayin magajin mahaifinsa ba tare da amincewar Olubadan ba.

A wani taro da aka yi a ranar 2 ga watan Maris, an kafa kwamiti don sanar da Olubadan na Ibadan kafin bikin nadin sabon Sarkin a lokacin addu’ar makoki.

Kara karanta wannan

'Ba ni ba neman sanata': Gwamna ya ce yana gama wa'adinsa zai yi ritaya a siyasa

Shugaban Sarakunan Arewa, Suleiman Rabiu, ya tabbatar da nadin, yana cewa shugabanni daga jihohi 17 sun halarci jana’izar da taron nadin magajin.

An gargadi Sarkin Hausawa kan kiran kansa mai iko
Olubadan a jihar Oyo ya ja kunnen sabon Sarkin Sasa bayan naɗinsa sarauta. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Twitter

Gargadin Olubadan ga sabon Sarkin Sasa

A madadin Sarkin, mai magana da yawun Olubadan, Gbenga Ayoade, ya ce Cif Akinade Ajani Amusa ne aka amince da shi a matsayin Baale na Sasa da hukuma ta san da shi.

Sanarwar ta bayyana cewa mutanen da ke zaune a yankin Sasa na karkashin ikon Baale Akinade Ajani Amusa wanda Olubadan ya amince da shi.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Dukkan mutanen Sasa su rika bin umarnin Baale Akinade Ajani, ya zama dole a ba shi girmamawa da ikon da ya dace.”
“Duk wanda ya saba wa umarnin Baale zai fuskanci hukunci mai tsauri, domin hakan raini ne ga kujerar Olubadan.”

Gwamna ya kare nadin babban Sarki

Kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya musanta cewa wasu sun yi ruwa da tsaki wajen zaben sabon Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade I.

Kara karanta wannan

'A tsaye aka karɓi ta'aziyya ta': Sheikh ya fadi dattakun ɗaliban Malam Dutsen Tanshi

Gwamna Makinde ya bayyana cewa Ifa ne ya zaɓi sabon Alaafin kamar yadda aka saba ba tare da wani ya zo wajensa domin tsoma baki ba.

Makinde ya bukaci mutane da masu adawa su marawa sabon Sarki baya, domin gujewa rikici da baraka a cikin garin Oyo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng