Babban Basaraken Igbo Ya Gargadi 'Yan Arewa kan Kisan Mafarauta a Edo? An Ji Gaskiya

Babban Basaraken Igbo Ya Gargadi 'Yan Arewa kan Kisan Mafarauta a Edo? An Ji Gaskiya

  • Babban basarake a ƙabilar Igbo, ya musanta batun cewa ya ja kunnen ƴan Arewa kan kisan da aka yi wa mafarauta 16 a Edo
  • Obi na Onitsha, Nnaemeka Achebe, ya ƙaryata rahotannin cewa ya yiwa ƴan Arewa gargaɗi kan ɗaukar fansa a kan Igbo
  • Mai martaban ya bayyana cewa rahotannin da aka yaɗa kan batun, babu komai a cikinsu face zallar ƙarya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Obi na Onitsha, Nnaemeka Achebe, ya yi magana kan batun cewa ya gargaɗi matasan Arewacin Najeriya kan kisan da aka yi wa mafarauta 16 a jihar Edo.

Mai martaba Nnaemeka Achebe ya ƙaryata cewa ya fitar da wata sanarwar gargaɗi ga matasan Arewa dangane da kisan mutanen da aka yi.

Obi na Onitsha, Nnaemeka Achebe
Nnaemeka Achebe ya musanta gargadin 'yan Arewa Hoto: WABMAfoundation
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa daga shugaban ma'aikatan fadar sarkin, Osita Anionwu, ya fitar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ndume ya tono fada kan sukar Tinubu, fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obi na Onitsa ya musanta gargaɗin ƴan Arewa

Ya bayyana cewa basaraken bai fitar da wata sanarwa ko yin tsokaci game da mummunan lamarin wanda ya faru a Uromi, ƙaramar hukumar Esan ta Arewa a jihar Edo, a ƙarshen watan Maris ba.

Nnaemeka Achebe ya bayyana rahotannin a matsayin ƙarya wacce aka shirya domin tayar da hankula, inda ya buƙaci jama’a da su yi watsi da su.

Sanarwar ta fito ne bayan wasu rahotanni sun mai martaba sarkin ya gargadi ƴan Arewa da kada su ɗauki matakin ramuwar gayya kan ƙabilar Igbo, sakamakon kisan mafarautan.

Me basaraken ya ce kan kisan mafarauta a Edo?

“Fadar Obi na Onitsha na sanar da jama’a cewa mai martaba, Nnaemeka Achebe (Agbogidi), bai fitar da wata sanarwa ba dangane da kashe wasu ƴan Arewa a jihar Edo. Haka kuma, bai yi gargaɗi ga kowa ba a kan lamarin."
“Wannan wani sabon misali ne na yadda ake ci gaba da danganta ƙarya ga mai martaba, domin tayar da husuma."

Kara karanta wannan

Iyalai da abokan mafarautan da aka kashe a Edo sun yi maganar daukar fansa

"Sanarwar da ake dangantawa da shi ba gaskiya ba ce, kuma tana da hatsari wajen haddasa rikici."
"Muna roƙon jama’a da su yi watsi da wannan ƙaryar da aka ƙirƙira, maimakon haka a mayar da hankali kan inganta zaman lafiya da fahimtar juna.”
“A matsayinsa na shugaban zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ƴan Najeriya, mai martaba yana da cikakkiyar niyyar samar da yanayi na mutunta juna da haɗin kai tsakanin mutane daga kabilu da yankuna daban-daban."

- Osita Anionwu

Gwamnatin Kano za ta tattauna kan kisan mafarauta

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ra tattauna da takwararta ta jihar Edo kan kisan da aka yi wa mafarauta 16.

Gwamnatin za ta yi tattaunawar ne kan adadin diyyar da za a biya iyalan mafarautan da aka yi wa kisan gilla a Uromi, ƙaramar hukumar Esan ta Arewa.

Tawagar da gwamnatin Kano za ta tura domin tattaunawar za ta kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamna, Aminu Abdulsalam Gwarzo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng