Pascal Dozie: Abubuwa 11 da Ya Kamata Ku Sani game da Attajirin da Ya Rasu a Najeriya
- A yau Talata, 8 ga watan Afrilu, 2025 aka samu labarin rasuwar attajirin ɗan kasuwa kuma shugaban MTN na farko, Pascal Gabriel Dozie
- Ɗansa ne ya sanar da rasuwar attajirin wanda ya kafa bankin Diamond kafin ya haɗe da bankin Access a shekarun baya-bayan nan
- Marigayin ya ba da gudummuwa matuka musamman lokacin da yake jagorantar kamfanin sadarwa mafi girma a Najeriya watau MTN
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tsohon shugaban kamfanin sadarwa watau MTN Nigeria kuma attajirin ɗan kasuwa, Pascal Dozie, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 85 a duniya.
An bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma wanda ya kafa tsohon bankin Diamond da yanzu ya haɗe da Access, Pascal Gabriel Dozie, a safiyar Talata, 8 ga Afrilu, 2025.

Asali: Twitter
Attajirin da ya kafa bankin Diamond ya rasu
Jaridar The Nation ta ce ɗansa, Uzoma Dozie, ne wanda ya fitar da sanarwar rasuwar mahaifinsa a madadin iyalansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Cike da alhini amma da godiya ga Allah kan rayuwa mai albarka, muna sanar da rasuwar mahaifinmu da mu ke kauna, Pascal Gabriel Dozie.”
Wannan dai babban rashi ne a Najeriya, sakamakon haka mun tattaro maku muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da tsohon shugaban MTN na farko a Najeriya.
Jerin abubuwa 11 game da Pascal Dozie
Ga su kamar haka:
1. An haifi Pascal Dozie a ranar 9 ga Afrilu, 1939, a garin Egbu da ke yankin Owerri, Babban birnin jihar Imo a kudu maso Gabashin Najeriya.
2. Ya rasu yana da shekara 85, kwana ɗaya tal kafin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, inda zai cika shekaru 86 a gobe Laraba, 9 ga watan Afrilun 2025.
3. Pascal Gabriel Dozie ya taso ne a gidan mabiya ɗarikar Katolika kuma mahaifinsa, Charles Dozie, ya kasance malami mai wa’azin addinin kirista.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi rashi, Attajirin da ya kafa bankin Diamond, ya jagoranci MTN ya rasu
4. Marigayin ya yi karatunsa na matakin farko a makarantun Our Lady’s School Emekuku, Holy Ghost Juniorate Seminary, da Holy Ghost College duk a Owerri.
5. Pascal Gabriel Dozie ya ci gaba da karatu a fannin Operational Research da Industrial Engineering, kafin daga bisani ya samu digiri na biyu a fannin Kimiyyar Gudanarwa daga Jami’ar City da ke London.
6. Marigayi Dozie ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban harkokin bankuna da sadarwa a Najeriya.
7. A shekarar 1990, ya kafa Diamond Bank, bankin da ya shahara a Najeriya kafin ya haɗe da bankin Access a ƴan shekarun da suka gabata.
8. Daga bisani Pascal Gabriel Dozie ya mika ragamar bankin ga ɗansa, Uzoma Dozie.
9. Ya kasance shugaban kamfanin sadarwa na MTN Nigeriana farko, inda ya taimaka wajen assasa ci gaban kamfanin da sauya tsarin sadarwa a ƙasar nan.
10. Salon jagorancinsa na gaskiya, tawali’u, da hangen nesa ya sanya aka karrama shi da lambar girmamawa ta ƙasa watau CON.
11. Marigayi Pascal Gabriel Dozie ya mutu ya bar mata ɗaya, Chinyere da ’ya’ya guda biyar.
Shugaba Tinubu ya yi ta'aziyyar Dozie
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban MTN Nigeria, Pascal Gabriel Dozie.
Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai, ‘yan kasuwa da kuma daukacin ‘yan Najeriya bisa rasuwar fitaccen attajiri kuma dattijon ƙasa.
Mai girma Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin gwarzon shugaba mai hangen nesa, wanda ya yi fice wajen gina tubalin ci gaban tattalin arziki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng