'Babu Hannun Kowa a Naɗinsa': Gwamna kan Naɗa Fitaccen Sarki Mai Daraja Ta 1

'Babu Hannun Kowa a Naɗinsa': Gwamna kan Naɗa Fitaccen Sarki Mai Daraja Ta 1

  • Gwamna Seyi Makinde ya musanta cewa wani ya shige gaba wajen zaben sabon Alaafin Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade I
  • Makinde ya bayyana cewa Ifa ne ya zaɓi sabon Alaafin, ba tare da wani ya zo wajensa domin tsoma baki cikin zaben ba
  • Gwamnan ya bukaci mutane da masu adawa su marawa sabon sarki baya, domin gujewa rikici da baraka a cikin garin Oyo
  • Sabon Alaafin, Oba Owoade I, ya godewa gwamnati da al'ummar Oyo, yana mai kiran hadin kai da goyon bayan jama'arsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde ya kalubalanci masu cewa akwai hannun wasu a nadin fitaccen Sarki.

Gwamnan ya caccaki duk masu cewa akwai wadanda suka tsoma baki wajen zaben sabon Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade I.

Kara karanta wannan

'Ba ni ba neman sanata': Gwamna ya ce yana gama wa'adinsa zai yi ritaya a siyasa

Gwamna ya yi magana kan nadin sabon Sarki a jiharsa
Gwamna Seyi Makinde ya ƙaryata hannun wasu a nadin Sarki Alaafin na Oyo. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Gwamna ya jaddada girman kujerar babban Sarki

Makinde ya fadi hakan ne yayin bikin nadin sabon Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade I, da aka gudanar a garin Oyo, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya jaddada cewa:

"Wadanda suka zo wajena domin tsoma baki ba su samu nasara ba, babu wanda ya zo domin tsoma baki, Ifa ne ya zaɓe shi."

Makinde ya bayyana muhimmancin sarautar Alaafin a al’adar Yarbawa, yana mai cewa ba abin sayarwa ba ce ko wani zai mallaka.

Ya bukaci Oyomesi da mutanen Oyo su marawa sabon Sarkin baya domin kaucewa irin rabuwar kawunan da aka fuskanta a baya da suka jawo matsaloli.

Makinde ya gargadi masu shirin kai kara kotu su tuna da shari'ar Eleruwa, wanda aka tube, amma daga baya mutanen gari suka dawo da shi.

Ya ce:

"Ka da su bata lokacinsu ko na jama’a, su hadu da sabon Alaafin wanda Allah, Ifa, mutanen Oyo da gwamnati suka zaba."

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, mai magana da yawun APC ya rasu a ƙasar waje

Gwamna ya musanta labarin da ake yaɗawa kan nadin Sarki
Gwamna Seyi Makinde ya kalubalanci masu ikirarin karya man nadin Alaafin na Oyo. Hoto: Oba Abimbola Akeem Owoade I.
Asali: Twitter

Sabon Sarki yabawa Gwamna kan goyon bayansa

A jawabinsa na karbar mulki, Oba Owoade I ya godewa Gwamna Makinde, gwamnatin jihar da al’ummar Oyo bisa goyon bayan da suka ba shi.

Ya ce:

"Wannan goyon baya yana kara karfin gwiwa da kwarin zuciya, yana sa mutum ya fuskanci kalubale ba tare da tsoro ba."

Sabon sarkin ya bukaci hadin kai da goyon bayan jama’arsa da mutanen Yarbawa domin samun ci gaba da zaman lafiya a masarautarsa, cewar Punch.

Oba Owoade I ya kara da ce:

"Hadewar al'umma na da karfin kawo sauyi mai ma’ana a cikin al’umma da ma kasarsa baki daya."

Gwamna ya mayar da Sarki bayan tsige shi

Kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya dawo da sarkin Eruwa, Prince Adebayo Adegbola kan sarauta bayan shekaru sama da biyar da tsige shi.

An tattaro cewa tun farko Mai martaba Adegbola ya hau kan sarautar Eleruwa na Eruwa a 1998 amma rikicin da ya biyo ya jawo tsige shi a 2019.

Kwamishinan yaɗa labarai na Oyo ya ce bayan shafe shekaru babu basarake a masarautar, Makinde ya yanke shawarar dawo da Adegbola.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng