N1629/$1: Ana Murna Fetur Ya Sauka, Dala Ta Tumurmusa Naira a Kasuwar Canji
- Darajar Naira ta kara faduwa, inda ta kai N1,629 kan kowacce dala a kasuwar NFEM duk da bankin CBN ya narka dala miliyan 688
- Naira ta kuma fadi a kasuwar bayan fage, domin ta sauka daga N1,565 zuwa N1,570, wanda ya sa bambancinta da NFEM ya karu zuwa N59
- Rahotanni sun nuna Naira ta fadi da kashi 2.4% a NAFEM da 2.6% a kasuwar bayan fage saboda yawan bukatar dala da rashin wadatarta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A jiya Litinin, 7 ga watan Afrilu, 2025, darajar Naira ta karye zuwa N1,629 kan kowacce dala a kasuwar musayar kuɗi ta Najeriya (NFEM).
An ce dalar Amurka ta tumurmusa Naira a kasuwar canjin duk da cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya antaya dala miliyan 688.8 a kasuwar don dakile hakan.

Asali: Getty Images
N1629/$1 Darajar Naira ta karye a kasuwar canji
Bayanan da CBN ya fitar sun nuna cewa farashin musayar Naira ya karu daga N1,600/$ a ranar Juma’a zuwa N1,629/$, wanda ke nuna ragin N29, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, naira ta fadi kasa warwar a kasuwar bayan fage inda ta karye daga N1,565/$ a karshen makon da ya gabata zuwa N1,570/$.
Sakamakon haka, bambanci tsakanin kasuwar bayan fage da farashin kasuwar NFEM ya karu daga N35 zuwa N59 a kan kowacce dala.
Bugu da ƙari, Naira ta karye da kashi 2.4% a kasuwar NAFEM da kuma 2.6% a kasuwar bayan fage a watan Maris, idan aka kwatanta da watan Fabrairu.
'Naira ta karye duk da matakin CBN' - AIICO
Rahoton wata-wata na Afrinvest mai take “Binciken tattalin arzikin duniya da Najeriya da kasuwannin kuɗi” ya nuna cewa Naira ta fadi kasa zuwa N1,536.82/$ a kasuwar NAFEM da N1,530/$ a kasuwar bayan fage.

Kara karanta wannan
An shiga murna da kayan abinci ya sauko a wasu jihohi 2, shinkafa ta koma N67,000
AIICO Capital ta kuma tabbatar da hakan a rahotonta na wata-wata, inda ta ce Naira ta fuskanci matsin lamba sosai a kasuwar musayar kuɗi.
“Darajar Naira ta karye sosai a watan Maris din 2025 saboda ci gaba da matsin lambar bukatar dala a kasuwar musayar kuɗi ta Najeriya,” inji rahoton AIICO Capital.
Channels TV ta rahoto AIICO ya fayyace cewa:
“Duk da cewa CBN ya narka dala $668.8m, darajar Naira ba ta wani samu tagomashi ba har aka kammala cin kasuwar, sai ma faduwa da ta yi da kashi 2.97%, inda ta sauka daga N1,492.49/$ zuwa N1,536.82/$."
Abin da ya jawo Dala ta tumurmusa Naira

Asali: Getty Images
A cewar AIICO Capital, bukatar dala ta kasance mai yawa musamman daga masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma kamfanoni na cikin gida.
Rahoton ya kuma nuna cewa kasuwar bayan fage ma ta bi sahun neman dala, inda darajar Naira ta sauka da kusan N43.50 zuwa N1,536/$.
Ko da yake CBN ya shigo da tallafin miliyoyin dala a tsakiyar watan, hakan bai hana bukatar kudin ta ci gaba da wuce abin da ake da shi ba.
Naira ta farfado a kasuwar canji
A wani labarin, mun ruwaito cewa, darajar Naira ta ɗan fardado, inda aka sayar da ita a kan N1,494.03/$ a kasuwar gwamnati da N1,510.00/$ a kasuwar bayan fage.
Wannan ya biyo bayan matakin Babban Bankin Najeriya (CBN) na tsawaita siyar da dala ga ‘yan canji har zuwa watan Mayun 2025 domin ƙarfafa wadatar kudin waje.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa suna bin tsare-tsaren kudi na zamani domin daidaita kasuwar musayar kuɗi da hana hauhawar farashi a ƙasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng