'Yan Bindiga Sun kai Hari kan Daliban Jami'a a Kebbi cikin Dare

'Yan Bindiga Sun kai Hari kan Daliban Jami'a a Kebbi cikin Dare

  • Wasu 'yan bindiga sun sace dalibi dan shekarar karshe a Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi (FUBK) a harin da suka kai da cikin dare
  • 'Yan ta'addar sun harbe wani mazaunin yankin, Malam Siddi Hussaini, har lahira yayin da ya fito domin duba shanunsa a lokacin harin
  • Shugaban jami’ar ya kai ziyara gidan hayar tare da jami’an tsaro, ya tabbatar wa daliban gwamnati za takare rayukansu da dukiyoyinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kebbi - Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kutsa wani gidan haya na dalibai da ke wajen harabar Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi (FUBK).

Rahotanni sun tabbatar da cewa a lokacin da suka kai harin, 'yan bindigar sun sace wani dalibi mai suna Augustine Madubiya.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya tsoma baki a rikicin sarautar Kano bayan janye gayyatar Sanusi II

Kebbi
An sace dalibin jami'a a jihar Kebbi. Hoto: Legit
Asali: Original

Rahoton Channels TV ya nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na daren Talata a Istijaba Villa da ke Unguwar Jeji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an kai harin ne a lokacin da daliban ke kwance a waje saboda tsananin zafi.

‘Yan bindiga guda biyar dauke da makamai ne suka bukaci kudi daga daliban, amma bayan an bayyana musu cewa babu, sai suka fara dukan su, inda daga baya suka sace daya a cikinsu.

An sace dalibi, an kashe mazaunin unguwa

A yayin da suka kai harin, wani mazaunin unguwar da ake kira Malam Siddi Hussaini ya fito domin duba shanunsa da ke kusa da wurin, amma ‘yan bindigar suka harbe shi har lahira.

Dalibin da aka sace mai suna Augustine Madubiya, na karatu a shekarar karshe a sashen tattalin arziki.

Sai kuma wani dalibi mai suna Collaneous Steven daga sashen gudanar da kasuwanci ya tsere daga hannunsu.

Kara karanta wannan

Kamar a Jahiliyya: An tono gawa bayan mahaifi ya kashe, ya birne 'yarsa a Najeriya

An tabbatar da lamarin ne bayan ziyarar da shugaban jami’ar, Farfesa Muhammad Zaiyan Umar, ya kai tare da DPO na Kalgo da jami’an DSS.

Farfesa Muhammad Zaiyan Umar ya tabbatar wa daliban cewa jami’ar za ta tabbatar da tsaro a yankin.

An bukaci ceto dalibin da aka sace

Farfesa Umar ya riga ya sanar da Gwamnan Jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ta hannun Sakataren Gwamnati da Daraktan Tsaro na ofishin majalisar zartarwa.

Jami’ar ta gode wa Hakimin Unguwar Jeji da mazauna yankin bisa taimako da goyon bayan da suka bayar yayin da ake kokarin shawo kan lamarin.

Kebbi
An bukaci gwamnati ta ceto dalibin da aka sace a Kebbi. Hoto: Nasir Idris
Asali: Twitter

Haka kuma, jami’ar ta bukaci taimakon gwamnati, rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin gano inda dalibin da aka sace yake da kuma kare faruwar irin haka a gaba.

An tarwatsa masu zanga zanga a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun tarwatsa wasu tarin matasa da suka fita zanga zanga a wasu biranen Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan mummunan hari da Bello Turji ya kai, ƴan bindiga sun kona makaranta kurmus

Matasa masu zanga zangar sun fito kan tituna a Abuja, Legas da wasu biranen kasar suna bukatar gwamnati ta magance matsalolin Najeriya.

Sai dai dama tun kafin fara zanga zangar, 'yan sanda sun gargadi matasan da cewa babu bukatar yin zanga zanga a ranar 'yan sanda ta kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng