Tinubu Ya Aiko Sako daga Faransa kan Mutuwar Shugaban MTN na Farko

Tinubu Ya Aiko Sako daga Faransa kan Mutuwar Shugaban MTN na Farko

  • Shugaba Bola Tinubu ya nuna jimaminsa kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa, Pascal Dozie, yana mai yabon gudunmawarsa ga ci gaban tattali
  • Mista Pascal Dozie wanda ya kafa bankin Diamond, ya kuma shugaban farko na MTN a Najeriya, ya rasu a yau yana da shekaru 85 a duniya
  • Tinubu ya bukaci 'yan kasuwa masu zaman kansu su ci gaba da gina Najeriya bisa jajircewa da gaskiya irin yadda marigayi Pascal Dozie ya yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Pascal Gabriel Dozie.

Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyya ga ‘yan kasuwa da kuma daukacin ‘yan Najeriya bisa rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijon ƙasa.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, Attajirin da ya kafa bankin Diamond, ya jagoranci MTN ya rasu

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya yi ta'aziyyar shugaban MTN na farko, Pascal Dozie. Hoto: Bayo Onanuga|Imran Muhammad
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ta'aziyar da Bola Tinubu ya yi ne a cikin wani sako da fadar shugaban kasa ta wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya ce marigayin ya bar tarihi mai zurfi wajen inganta harkokin kasuwanci da tsarin banki da sadarwa a Najeriya.

Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin gwarzon shugaba mai hangen nesa, wanda ya yi fice wajen gina tubalin ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Bola Tinubu ya fadi gudumawar Pascal Dozie

Tinubu ya tabbatar da cewa Dozie ne ya kafa bankin Diamond, daya daga cikin manyan bankuna a Najeriya kafin a hade shi da bankin Access.

Haka kuma, marigayin ya kasance shugaban farko na kamfanin MTN Nigeria, kamfanin sadarwa mafi girma a ƙasar.

A cewar shugaba Tinubu, Dozie ya kasance ginshiki wajen samar da sababbin hanyoyin kasuwanci da samar da ingantaccen sadarwa da ayyukan banki.

Tinubu ya ce:

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya kaɗu da Allah ya yi wa tsohon gwamna rasuwa a Najeriya

“Pascal Dozie na daya daga cikin 'yan kasuwa da suka gina tubalin da yawancin mutane ke ci gaba da dorawa a kai har yau.”

Aikin da Dozie ya yi a bankin CBN

Baya ga nasarorinsa a fannin kasuwanci, Dozie ya taba zama darakta a Babban Bankin Najeriya (CBN).

Haka zalika ya taba zama shugaban kasuwar hada-hadar hannayen jari (NSE), da kuma shugaban majalisar tattalin arzikin kasa (NESG).

Haka kuma, ya taka rawa wajen tsara manufofin gwamnati da habaka harkokin 'yan kasuwa masu zaman kansu da karfafa matasa.

Tinubu
Tinubu ya nuna damuwa kan mutuwar wanda ya kafa bankin Diamond. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Tinubu ya yaba da hikimar marigayin da yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen inganta ƙasa, yana mai cewa wannan babban rashi ne ga fannin kasuwanci da kuma Najeriya baki ɗaya.

A karshe, shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan Pascal Dozie ya kuma bai wa iyalansa juriya da ƙarfin zuciya.

Malamin addini, Sheikh Yahya Harun ya rasu

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisa ya dura kan Tinubu da Shettima saboda ficewa Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa wani fitaccen malamin Musulunci a jihar Gombe, Sheikh Yahya Harun ya rasu.

Legit ta rahoto cewa marigayin ya kasance cikin manyan malaman jihar Gombe kuma shi ne babban limamin Juma'a a barikin 'yan sanda da ke jihar.

Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana rasuwar Sheikh Yahya Harun a matsayin babban rashi lura da irin gudumawar da yake ba wa addini.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel