Ana Shirin Fara Aikin Hajji, Sabon Rikici Ya Ɓarke a Hukumar Alhazan Najeriya
- Ana shirin fara jigilar alhazai, rikici ya kunno kai a NAHCON, inda kwamishinoni suka koka da salon shugabancin Abdullahi Saleh Usman
- Kwamishinonin sun aika korafi ga Kashim Shettima, suna zargin shugaban NAHCON da karya ƙa’idoji, da ware su daga harkokin hukumar
- Sun ce an ware su daga ayyukan hukumar, ciki har da tafiyar duba wuraren Hajji da tsara kuɗin kujera, inda suka nemi a saurare su da gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kasa da wata guda kafin fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya domin aikin Hajjin 2025, rikici ya ƙara ɓarke a hukumar Hajji ta kasa (NAHCON).
Rahotanni sun nuna cewa 'yan kwamitin gudanarwar hukumar sun nuna rashin jin daɗi da irin salon mulki na shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa waɗanda ke cikin wannan rikici, waɗanda kuma su ke matsayin kwamishinonin NAHCON, sun rubuta takardar korafi zuwa ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinonin NAHCON sun kai kara ga Shettima
A cikin takardar korafin, sun zargi shugaban hukumar da manyan laifuffuka na rashin da'a, karya ƙa'idojin saye da sayarwa, da kuma ware su daga harkokin hukumar gaba ɗaya.
Takardar korafin da jaridar ta gani na zuwa ne makonni bayan kungiyar ma'aikatan NAHCON ta zargi hukumar da rashin kula da walwalar su, zargin da hukumar ta karyata.
Dukkan 'yan kwamitin gudanarwar NAHCON daga shiyyoyi shida, tare da wakilai biyu daga majalisar koli ta harkokin Musulunci (NSCIA) da kuma kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), sun sa hannu a takardar.
Har yanzu ba a samu tabbacin ko ofishin mataimakin shugaban kasa ya karɓi takardar ba, domin kakakin Shettima, Stanley Nkwocha, bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka tura masa ba.
Sunayen kwamishinoni 8 da suka kai karar
Sai dai wasu daga cikin waɗanda suka rattaba hannu a takardar sun tabbatar wa da manema labarai cewa takardar ta kai ga ofishin mataimakin shugaban kasar.
Waɗanda suka sa hannu a takardar korafin sun haɗa da:
- Farfesa Muhammad Umaru Ndagi (Arewa ta Tsakiya)
- Alhaji Abba K. Jato (Arewa Maso Gabas)
- Sheikh Muhammad Bn Uthman (Arewa Maso Yamma)
- Hajiya Aishat Obi (Kudu Maso Gabas)
- Hajiya Zainab Musa (Kudu Maso Kudu)
- Dr Tajudeen Abefe Oladejo (Kudu Maso Yamma)
- Farfesa Adedimeji Mahfouz Adebola (NSCIA)
- Farfesa Musa Inuwa Fodio (JNI)
Sai dai hukumar NAHCON ta bayyana cewa dukkanin ayyukanta na tafiya ne bisa ƙa'ida kuma babu wani da ake warewa kamar yadda aka zarga.
Farfesa Abdullahi Usman ya hau kujerar shugabancin NAHCON ne a watan Agusta 2024, bayan nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi masa, wanda ya maye gurbin Jalal Ahmad Arabi.
Korafe-korafe kan shugaban hukumar NAHCON

Asali: Twitter
Masu korafin sun bayyana cewa an ware su daga tafiyar duba wuraren Hajji a Saudiyya, ƙayyade kuɗin Hajji, zaɓen masu kula da alhazan Najeriya a Saudiyya, da sauran aikace-aikace na sa ido.
Haka kuma sun zargi shugaban da yin kaka gida wajen wajen tafiyar da harkokin kudi, musamman wajen ware su a sha'anin ba da kwangilar saye-sayen kayayyaki.
Waɗannan kwamishinoni guda takwas waɗanda ba na dindindin ba ne, sun ce shugaban Farfesa Usman yana kawo masu wargi saboda haƙuri da dattakon da suke nuna masa.
Sun ƙara da cewa ba a taɓa bai wa wakilai daga shiyyoyi da kuma NSCIA da JNI damar wakiltar yankunansu ba tun daga lokacin naɗinsu.
NAHCON ta sanya lokacin fara jigilar alhazai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shirye-shiryen jigilar maniyyatan Najeriya domin aikin Hajjin 2025 na ci gaba da gudana cikin tsari a hukumar NAHCON.
Hukumar ta bayyana cewa za a fara jigilar alhazan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki a cikin watan Mayun shekarar nan.
A cewar NAHCON, an zaɓi kamfanonin jiragen sama guda huɗu da za su ɗauki nauyin jigilar maniyyata zuwa Saudiyya domin aikin Hajji.
Asali: Legit.ng