Ajali Ya Yi: Fitattun Mawaƙa 4 a Najeriya Sun Mutu a Mummunan Hatsarin Mota
- Mawakan yabo na addinin kirista guda hudu sun rasa rayukansu a wani hatsarin motoci da ya rutsa da su a jihar Ogun
- Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Ogun ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce hatsarin ya faru ne saboda gudun wuce kima
- Tuni dai mabiya addinin kirista suka fara miƙa sakon ta'aziyya da jimamin wannan rashi na fitattun mawaƙa huɗu a lokaci guda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ogun - Rahotanni sun tabbatar da mutuwar fitattun mawakan yabo na addinin kirista su hudu sakamakon mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a jihar Ogun
Mawakan masu wakokin yabo a coci sun rasa rayukansu ne a wani hatsari da ya afku a kan titin Ikorodu-Sagamu da ke jihar Ogun.

Asali: Original
Kakakin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Ogun, Florence Okupe, ta tabbatar da lamarin a wata sanarwa da ya fitar, Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan
"Najeriya za ta shiga rudani," JNI ta ja kunnen gwamnati kan kisan kiyashi a Filato da Kebbi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda suka rasu sun hada da, Evangelist Ayodeji Kekerejesu, Evangelist Iyanu Joseph, Monjolajesu Oluwapamilerin da Opeyemi Adesina.
Yadda hatsari ya lakume rayukan mawaka 4
Sanarwar ta bayyana cewa hadarin ya afku ne bayan motar da ke dauke da mawakan ta yi karo da wata mota a hatsari mai muni da ya ritsa da motocin da dama.
Okupe ta kara da cewa dukkan mawakan da suka rasu ’yan gida daya ne, kuma sun rasu a nan take a wurin da hatsarin ya afku.
Wannan lamarin ya girgiza masana’antar waƙoƙin yabo ta Najeriya, inda mutane da dama ke bayyana alhini da jimami bisa rasuwar matasa da ke da gagarumin tasiri a harkar waƙoƙin addini.
An fara alhinin rasuwar mawaƙan
Shugaban cocin Christ Apostolic, Fasto Sam Olu Alo, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi a wata sanarwa da ya fitar.
Limamin cocin ya ce:
"Allah kenan mai yadda ya so, wannan babban tashin hankali ne a yau. Amma wa za mu tuhuma? Ƙaddara ta fi ƙarfin mu."

Kara karanta wannan
"Abin tausayi": Mutane sun yi magana, an ji yadda aka kashe bayin Allah sama da 50

Asali: Facebook
Me ya haddasa hatsarin mawakan addini?
Rahoton hukumar FRSC ya bayyana cewa hadarin ya faru ne sakamakon taho mu gamar motoci da ya faru tsakanin motar da ke dauke da mawakan da wata mota.
An ruwaito cewa hadarin ya rutsa da motoci da dama tare da hallaka fiye da mutane 24.
Binciken farko ya nuna cewa gudu fiye da kima da kuma rashin gani da kyau hanya ne suka haddasa wannan hadari mai muni.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an riga an birne gawarwaki biyu daga cikin mawakan yayin da sauran aka tafi da su Ado-Ekiti domin yi masu jana'iza.
Jam'iyyar PDP ta yi rashin babban jigo a Oyo
A wani labarin, kun ji cewa jigon PDP kuma Seriki Musulmi na ƙasar Yarbawa, Alhaji Yekini Ayoade Adeojo, ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin, wanda ya riƙe kujerar mataimakin shugaban PDP na ƙasa (Kudu) ya rasu ne da safiyar Juma'a a gidansa da ke Ibadan a jihar Oyo.
Gwamna Seyi Makinde ya miƙa sakon ta'aziyya bisa wannan babban rashi da jihar Oyo tayi, tare da fatan Allah Ya jiƙansa.
Asali: Legit.ng