Ana cikin Karbar Ta'azziya, Iyalan Dutsen Tanshi Sun Sake Gargadi kan Wasiyyarsa
- Dalibai da iyalan marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi sun sake fitar da sanarwa, suna jan hankalin al'umma kan wasiyyar da aka bari
- Magadan sun gargadi jama’a da su guji daukar hotuna ko bidiyo a wurin ta'aziyya sannan su daina yadawa a kafafen sada zumunta na zamani
- Sun bayyana cewa Sheikh Dutsen Tanshi tun yana raye yana Allah-wadai da masu yada hotonsa ko bidiyo a kafafen sadarwa ba tare da izini ba
- A cikin sanarwar da aka wallafa a Facebook, sun sake nanata cewa ba a yarda da daukar hoto ko bidiyo wajen ta’aziyya ba, aka bukaci a kiyaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Dalibai da iyalan marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi sun sake fitar da sanarwa bayan mutuwar malam.
Ɗaliban sun gargadi mutane da ke ci gaba da daukar hotuna ko bidiyo suna yaɗawa da su guji yin haka.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Dutsen Tanshi Majlis Bauchi ya wallafa a Facebook a daren jiya Litinin 8 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasiyyoyin marigayi Malam Idris Dutsen Tanshi
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar Malam Idris Dutsen Tanshi a daren ranar Juma'a 4 ga watan Afrilun 2025.
Tun kafin gudanar da jana'izar, dalibai da iyalan malam sun fitar da sanarwa kan wasiyyar da marigayin ya bari.
Daga ciki akwai haramta daukar hoto ko bidiyo musamman a lokacin sallar jana'izarsa a yada a kafofin sadarwa.
Tun yana raye, ya kuma ja Allah ya isa ga wadanda suke saukar hotonsa suke yaɗawa a kafofin sadarwa.
Yadda marigayi Dutsen Tanshi ya cika da imani
An tabbatar da cewa malamin ya cika da kalmar shahada a daren da ya bar duniya wanda ke nuna ya yi karshe mai kyau.
Wani matashi da ke tare da Sheikh Idris Abdulaziz a lokacin rasuwarsa ya bayyana yadda lamarin ya faru a gidansa da ke Bauchi.
Matashin ya ce a gabansa Sheikh Idris ya cika, suna cikin daki tare da ɗansa Muhammad lokacin da marigayin ya ambaci kalmar shahada.

Asali: Facebook
An sake gargadi kan hotunan Dutsen Tanshi
A cikin sanarwar, sun kuma ja kunnen mutane domin kiyaye dokokin da aka gindaya game da daukar hoto.
Sun gargadi al'umma su kiyayi daukar hotuna da bidiyo tare da kuma yadawa a kafofin sadarwa.
Sanarwar ta ce:
"Sanarwa/Janhankali.
"Daga yanzu ba mu yarda da dauke-dauken hotuna/bidiyo wajen ta'aziyar Dr. ba ana yadawa a kafofin sadarwa.
"Mu kiyaye."
Gwamna Bala ya ziyarci gidan marigayi Dutsen Tanshi
Kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalai da daliban marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi a Bauchi.
Gwamna Bala ya bayyana marigayin a matsayin gwarzon malami mai tsayawa kan gaskiya da bin koyarwar addinin musulunci ba tare da tsoro ba.
Sanata Bala Mohammed ya dauki alwashin mika filin idi na 'Games Village' domin amfanin daliban marigayin bayan rasuwarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng