Kudin Fansa: Hedkwatar Tsaro Ta Fito da Bayanin Yadda Aka Ceto Janar Tsiga

Kudin Fansa: Hedkwatar Tsaro Ta Fito da Bayanin Yadda Aka Ceto Janar Tsiga

  • Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana takaicin yadda ake yaɗa rahotannin da ke cewa an biya kuɗin fansa kafin a ceto tsohon shugaban hukumar NYSC
  • Wasu ’yan bindiga ne suka sace Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) daga gidansa da ke jihar Katsina kusan watanni biyu da suka gabata
  • Bayan an ceto shi ne, wani Birgediya Janar Ismaila Abdullahi (rtd) ya wallafa cewa shi ne ya jagoranci tattara kuɗin da aka biya domin ceto abokinsu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaHedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta karyata rahotanni da ke cewa an biya kudin fansa kafin ceto tsohon shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (rtd).

DHQ ta ta ce babu kamshin gaskiya a rahotannin da ke yawo kan cewa sai da aka biya miliyoyin Naira ga masu garkuwa da mutane kafin su sako Janar Tsiga bayan makonni.

Kara karanta wannan

Hajji 2025: Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan zargin hana ƴan Najeriya shiga Saudiyya

Janar
DHQ ta karyata biyan kudin fansa kafin ceto Janar Tsiga Hoto: Yarima Bk Dtm/Muhammad Aminu Kabir
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa an ceto Janar Tsiga ne ta hanyar wani aiki na bincike da ceto da dakarun Operation Fansan Yamma suka gudanar a yankin Arewa maso Yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ne a ranar Alhamis ya miƙa Janar Tsiga da sauran mutane 18 da aka ceto ga iyalansu a Abuja.

An biya kuɗi domin fansar Janar Tsiga?

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an sace Janar Tsiga a ranar 5 ga Fabrairu, 2025, a garinsa na Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina tare da wasu mutum tara.

Sai dai bayan ceto shi da sada Janar Tsiga da iyalansa, Birgediya Janar Ismaila Abdullahi (rtd) ya yi rubuce rubuce kan yadda aka tattaro kudin fansar tsohon babban jami'in sojan.

Janar
Janar Tsigatare da NSA, Nuhu Ribadu bayan ceto shi daga hannun 'yan bindiga Hoto: Muhammad Aminu Kabir
Asali: Facebook

A cewar Janar Abdullahi mai ritaya, shi ne ya jagoranci tara kuɗin da abokan Janar Tsiga suka bayar, wanda aka yi amfani da su wajen biyan kuɗin fansa domin a sake shi.

Kara karanta wannan

Tinubu na dab da sakawa Shehu Sani, Omokri da wasu 'yan adawa da mukamai

Martanin sojoji kan biyan fansar Janar Tsiga

Sai dai Babban hafsan tsaro na kasa, ta bakin Daraktan yaɗa labaran soji, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya karyata wannan ikirari a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa a daren ranar da aka sace Janar Tsiga da sauran mutane, dakaru suka samu kiran gaggawa kuma sun amsa nan take da misalin 3.00 na dare.

A cewar sanarwar:

“Ko da yake ba a samu yin arangama kai tsaye da masu garkuwar ba, dakarun sun matsa lamba sosai ga miyagun, lamarin da ya sa suka tsere suna barin dabbobin da suka sace da kuma wasu daga cikin mutanen da suka kama.
Duk da haka, dakarun sun ci gaba da bin sawun 'yan ta’addan ba tare da gajiya wa ba, kodayake sun fuskanci matsaloli saboda mawuyacin yanayin ƙasa.”

Yadda aka ceto Janar Maharazu Tsiga

Hedikwatar ta bayyana cewa daga bisani an kai farmakin sama a tsaunin Dunya, wanda ake zargin mafakar 'yan ta’adda ce kuma inda Janar Tsiga ke tsare.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 50, gwamna ya gano waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'adi

Wannan al'lamarin ya tayar da hankalin 'yan bindigar har wasu daga cikin fursunoni suka samu damar tserewa.

Sai dai sanarwar ta ce, abin bakin ciki shi ne tsohon shugaban NYSC ɗin bai iya tserewa ba saboda matsalolin lafiya da yake fama da su.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“A wani mataki na daban, dakaru sun kai farmaki a tsaunin Pauwa da yankin Matallawa da ke ƙaramar hukumar Kankara, domin cigaba da neman Birgediya Janar Tsiga.
“Amma dai, a lokacin, sun samu nasarar ceto mutane 84 da aka yi garkuwa da su daga yankin, ba tare da gano inda Janar ɗin yake ba. A lokacin farmakin, an kashe wasu 'yan bindiga yayin da sojoji uku suka samu raunin harbin bindiga.”

Sanarwar ta ƙara da cewa tun daga ranar da aka sace Janar Tsiga, dakaru ba su daina fafutuka ba, suna kai hare-hare a dazuka daban-daban.

Hare-haren sun matsa wa masu garkuwa da shi lamba, har aka samu nasarar ceto shi bayan an shafe tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

An fara gargadin gwamnatin Tinubu kan hana shigo da kayan sola Najeriya

Yadda 'yan ta'adda su ka sace Janar Tsiga

A baya, kun samu labarin cewa wasu fitsararrun ’yan bindiga sun sace tsohon shugaban hukumar NYSC na ƙasa, Birgediya Janar Maharazu Tsiga (rtd) har gidansa da ke Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa sace Janar Tsiga ya tayar da hankalin mazauna garin Tsiga na karamar hukumar Bakori. tare da jefa su cikin tsananin tsoro da rashin tabbas kan tsaronsu.

Bayanai sun nuna cewa, bayan sace tsohon shugaban na NYSC, mutane da dama sun fara barin gidajensu, suna tserewa domin gujewa wani mummunan hari daga ’yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.