Hajji 2025: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Bayani kan Zargin Hana Ƴan Najeriya Shiga Saudiyya

Hajji 2025: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Bayani kan Zargin Hana Ƴan Najeriya Shiga Saudiyya

  • Ma'aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta musata raɗe-raɗin da ke yawo na hana ƴan Najeriya shiga Saudiyya ana dab da fara tafiya hajji
  • Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar ya musanta jita-jitar, yana mai cewa Saudiyya ba ta hana ƴan Najeriya shiga kasar ba
  • Tuggar ya kuma bukaci ƴan Najeriya musamnan matafiya su daina ɗaukar kowane irin labari matuƙar ba daga hukumomi suka fito ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta karyata jita-jitar da ake cewa an hana ’yan Najeriya shiga Saudiyya.

Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a hana ’yan Najeriya shiga Saudiyya daga ranar 13 ga Afrilu, 2025.

Amabasada Yusuf Tuggar.
Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar hana yan Najeriya shiga Saudiyya Hoto: @Alkayy
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan harkokin watsa labarai, Alkasim Abdulkadir ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: Hedkwatar tsaro ta fito da bayanin yadda aka ceto Janar Tsiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jita-jitar Saudiyya ta hana kasashe shiga cikinta

Wannan dai na zuwa ne bayan wata takardar da ta bazu a kafafen sada zumunta, ta yi ikirarin cewa hukumomin Saudiyya sun hana kasashe cikin har da Najeriya shiga ƙasar.

Jita-jitar ta zo ne a daidai lokacin da maniyyata a Najeriya da sauran kasashen duniya ke shirye-shiryen tafiya Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin ɓana 2025.

An hana ƴan Najeriya shiga kasar Saudiyya?

Da yake musanta raɗe-radin, Alkasin ya ce takardar da ke yawo da ke nuna cewa Saudiyya ta dakatar da kasashe da dama ciki har da Najeriya, daga shigar cikinta ba gaskiya ba ce.

“Wannan takarda karya ce, kuma hukumomin Saudiyya sun riga sun musanta sahihancinta,” in ji Alƙasim

Ya ce cibiyar yawon buɗe ido ta Saudiyya ta ce dokar da ke aiki yanzu ba ta hana kowace ƙasa shiga ƙasar ba sai dai ta shafi masu bizar yawon shakatawa ne kawai a lokacin aikin Hajji.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban ƙasa ta yi maganar batun tsige shugaban INEC, Mahmud Yakubu

“Masu bizar yawon shakatawa ba su da damar shiga Makkah daga ranar 29 ga Afrilu zuwa 11 ga Yuni, 2025. Bizar Hajji ce kaɗai za a amince da ita a wannan lokaci,” in ji shi.
Yusuf Tuggar.
Ma'aikatar harkokin waje ta yi bayani kan zargin hana ƴan Najeriya zuwa Saudiyya Hoto: @NigeriaMFA
Asali: Twitter

Gwamnatin Najeriya ta ba matafiya shawara

Ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya ta kuma shawarci ’yan Najeriya da su daina yarda da labaran da ba su fito daga hukumomi ba, domin hakan na iya janyo rudani da katse shirye-shiryen tafiya.

“Jama’a musamman matafiya su tabbata suna karɓar bayanai daga hukumomin Saudiyya, Ma’aikatar Harkokin Waje ko ofisoshin jakadanci kafin su ɗauki kowanne mataki."

- In ji Alkasim Abdulkadir, hadimin ministan harkokin waje.

NAHCON za ta fara jigilar maniyyata

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya watau NAHCON ta kammala shirye-shiryen fara jigilar maniyyata zuwa ƙasar Saudiyya.

NAHCON ta bayyana cewa shiri ya yi nisa kuma ta tsara fara kwashe maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki daga watan Mayun 2025.

Saudiyya za ta buɗe sararin samaniyarta domin karɓar maniyyata daga ranar 29 ga watan Afrilu, kuma jirgin farko daga Najeriya zai tashi a ranar 6 ga watan Mayu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng