Ministan Tinubu Ya ba da Mamaki, Ya Ce Ya Shirya Shiga Zanga Zangar Matasa a Najeriya

Ministan Tinubu Ya ba da Mamaki, Ya Ce Ya Shirya Shiga Zanga Zangar Matasa a Najeriya

  • Ministan matasa na kasa, Kwamared Ayodele Olawande ya ce rashin lokaci ke hana shi shiga zanga-zangar matasa a Najeriya
  • Kwamared Olawande ya gargaɗi matasa da su guje wa tayar da tarzoma ko lalata kayan gwamnati yayin zanga-zangar da suke yi
  • Ya ce gwamnatin tarayya ba za ta hana jama'a yin zanga-zanga ba amma kuma a shirye take da saurari kokensu cikin lamana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan harkokin matasa na Najeriya, Kwamared Ayodele Olawande ya ce rashin lokaci ya hana shi shiga zanga-zangar da matasa ke yi a Najeriya.

Ministan ya bayyana cewa da yana da isasshen lokaci, zai shiga cikin matasa masu zanga-zangar da aka fara yau Litinin ƙarƙashin kungiyar Take It Back.

Ministan matasa, Ayodele Olawande.
Ministan matasa ya ce gwamnati ba ta hana matasa yin zanga-zanga ba Hoto: Ayodele Olawande
Asali: Facebook

Kwamared Olawande ya faɗi haka ne da yake zantawa da manema labarai a wurin taron shekara-shekara na matasa masu yi wa kasa hidima watau NYSC a Abuja, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Matasa sun bijirewa ƴan sanda, sun mamaye titunan Abuja da wasu jihohi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya bukaci matasan Najeriya su fito su bayyana abin da ke ransu amma ya gargaɗe su da su guji lalata kayayyakin gwamnati da sunan zanga-zanga.

Matasa sun fara zanga-zanga a Najeriya

Wannan kalamai na Kwamared Ayodele Olawande na zuwa ne a daidai lokacin da zanga-zanga ta ɓarke a Abuja, Legas da wasu jihohi yau Litinin, 7 ga watan Afrilu.

Zanga-zangar da ƙungiyar 'Take It Back' ta shirya na ci gaba da gudana duk da gargaɗin da rundunar ‘yan sanda ta yi a kan gangamin.

Tun farko dai rundunar ‘yan sanda ta ce ba ta yarda da zanga-zangar ba, kasancewar an shirya ta a ranar da gwamnati ta ware don bikin 'Ranar ‘Yan Sanda ta Ƙasa'.

Minista ya ce zai shiga iya zanga-zanga

Da yake hira da ƴan jarida kan lamarin, Ministan ya ce matasa na da 'yancin bayyana ra’ayoyinsu, sai dai ya ja kunnen su cewa kada su tayar da zaune tsaye ko lalata kayayyakin gwamnati.

Kara karanta wannan

Matasa sun rikita Abuja da zanga zanga, an fara harba barkonon tsohuwa

“Duk wanda ke da damuwa kan halin da ake ciki yana da 'yancin yin zanga-zanga. Da zan samu lokaci, da na je na halarci wannan zanga-zangar,” in ji shi.

Ya ce babu gwamnatin da za ta hana mutane yin zanga-zanga, kuma za a saurari koke-koken su.

Ministan matasa.
Ministan Tinubu ya gargaɗi matasa kan tayar da hankali a lokacin zanga-zanga Hoto: Ayodele Olawande
Asali: Twitter

Wane gargaɗi ministan ya yi wa matasa?

Duk da haka, ya gargaɗi matasa da su kauce wa tashin hankali da lalata kadarorin gwamnati, musamman waɗanda lalacewarsu za ta shafi tattalin arzikin ƙasa.

“Ina tare da su, kuma zan je in yi magana da su idan na samu lokaci,” in ji Olawande.

Ya ƙara da cewa gwamnati a shirye take ta saurari muradun matasa tare da neman mafita cikin lumana.

Abin da ƴan sanda suka yi wa masu zanga-zanga

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya watau Amnesty Int'l, ta koka kan yadda jami'an tsaro ke farmakar masu zanga-zanga.

Kara karanta wannan

'Ba ni ba neman sanata': Gwamna ya ce yana gama wa'adinsa zai yi ritaya a siyasa

Ƙungiyar ta bayyana matuƙar damuwa da yadda jami’an tsaro ke cin zarafin masu zanga-zanga a Abuja da Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Ta ce a Fakwal, ƴan sanda sun rika dukan masu zanga-zanga da ƴan jarida, sannan kuma sun fesa masu barkono mai sa hawaye.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel