Shugaba Tinubu Ya Tsige Shugaban INEC kuma Ya Naɗa Sabo? Gaskiya Ta Bayyana
- Hukumar zaɓe ta ƙasa watau INEC ta musanta rahoton da mutane ke yaɗawa cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tsige Mahmud Yakubu
- INEC ta buƙaci ƴan Najeriya su yi fatali da wannan rahoto domin babu kanshin gaskiya a cikinsa kuma shugabanta na nan daram a muƙaminsa
- A tsarin doka, kafin shugaban kasa ya naɗa shugaban hukumar zaɓe, sai ya bi wasu matakai wanda ya haɗa da tantancewar hukumar DSS
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta musanta jita-jitar da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa Bola Tinubu ya tsige shugabanta, Farfesa Mahmud Yakubu.
Hukumar INEC ta karyata wannan jita-jita da ake yaɗawa, tana mai cewa Farfesa Mahmud Yakubu na nan daram a muƙaminsa.

Asali: Twitter
Yadda aka fara yaɗa labarin tsige shugaban INEC
Wani sako da ake ta yaɗawa shafukan sada zumunta na Whatsapp, Facebook da X ciki har da shafin Naija, ya yi ikirarin cewa Tinubu ya canza Mahmud Yakubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saƙon ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauke Farfesa Mahmud daga shugabancin INEC kuma ya maye gurbinsa da wani Farfesa Bashiru Olamilekan
A cikin saƙon wanda bai da wani tushe ba, ya ce:
"Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sauke shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, kuma ya maye gurbinsa da Farfesa Bashiru Olamilekan.”
Da gaske Tinubu ya tsige shugaban INEC?
Sai dai hukumar INEC ta fito ta karyata wannan labari, tana mai cewa babu ƙanshin gaskiya a cikinsa.
Da yake ba da amsa yayin da jaridar Vanguard ta tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama'a na ofishin shugaban INEC, Mista Rotimi Oyekanmi ya buƙaci ƴan Najeirya su yi watsi da jita-jitar.
Oyekanmi, ya ce:
“Don Allah ku yi watsi da wannan jita-jita. Ba gaskiya ba ne.”
Farfesa Mahmud Yakubu, wanda ke cikin wa’adi na biyu a shugabancin hukumar INEC, ana sa ran zai bar ofis a ƙarshen wannan shekara da muke ciki watau 2025.
Matakan naɗa sabon shugaban INEC
A tsarin nadin sabon shugaban INEC, Shugaban Kasa ne ke zabar wanda zai maye gurbin, sannan ya mika sunan wanda ya zaɓa ga Hukumar Tsaro ta DSS don tantancewa.
Bayan an kammala tantancewa, Shugaban Kasa zai kai sunan ga Majalisar Dattawan Ƙasa da ta ƙunshi tsofaffin shugabannin ƙasa don neman shawarwari.
Daga nan kuma shugaban zai tura sunan ga Majalisar Dattawa don tantancewa da tabbatarwa.
INEC ta tura saƙo Majalisa kan Natasha
A wani rahoton, kun ji cewa INEC ta sanar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio cewa buƙatar tsige Natasha Akpoti-Uduaghan ba ta cika ƙa'idojin doka ba.
INEC ta ce ta yi nazari kan sa hannun masu bukatar korar sanatar daga mazaɓarta amma ba su kai adadin da kundin tsarin mulki ya tanada ba.
Wannan dai na zuwa ne bayan wasu mutanen Kogi ta Tsakiya sun nemi yi wa Natasha kiranye sakamakon abubuwan da ta yi a Majalisar Dattawa.
Asali: Legit.ng