Shugaba Tinubu Ya Kaɗu da Allah Ya Yi wa Tsohon Gwamna Rasuwa a Najeriya
- Mai girma Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon gwamnan jihar Oyo, Dr. Victor Omololu Olunloyo
- Tsohon gwamnan ya rasu ne ranar Lahadi, 6 ga watan Afrilu, 2025 saura ƴan kwanaki ya cika shekaru 90 a duniya
- A sakon da ya aika a madadin gwamnatin tarayya, Tinubu ya ce marigayin ya ba da gudummuwa wajen bunƙasa ilimi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnatin da al’ummar jihar Oyo bisa rasuwar tsohon gwamna, Dr. Victor Omololu Olunloyo.
Shugaba Tinubu ya yi jimamin wannan rashi tare da miƙa ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan marigayi tsohon gwamna na tsohuwar jihar Oyo.

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta tattaro cewa Tinubu ya yi jimamin wannan rashi ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar ranar Lahadi.
A madadin gwamnatin tarayya, Shugaba Tinubu ya mika ta’aziyya ga dangin Olunloyo, ƴan uwa da dukkanin wadanda suka san shi a matsayin dattijo kuma kwararren malami.
Taƙaitaccen bayani kan tsohon gwamnan Oyo
Marigayi Olunloyo ya shahara a fannin lissafi, inda ya samu digirin digirgir (PhD) a fannin “Applied Mathematics” da “Number Theory” daga jami’ar St. Andrews da ke Scotland yana da shekaru 25.
A shekarar 1962, yana da shekaru 27 kacal, ya zama kwamishina a tsohuwar jihar Yammacin Najeriya, kuma ya yi ayyuka da dama a jihar Yamma bayan an sake tsara yankin.
Ya kuma kafa tubalin ci gaban ilimi da shugabanci a matsayin babban darakta na farko na Kwalejin Fasaha ta Ibadan da ta Jihar Kwara.
Tinubu ya faɗi gudummawar marigayin
Shugaba Tinubu ya bayyana Dr. Olunloyo a matsayin mutum mai hazaka, wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga ci gaban ilimi da kasa baki daya.
“Za a ci gaba da tunawa da Dr. Olunloyo a duniyar ilimi saboda gudunmawar da ya bayar a fannin kimiyyar lissafi.
"A matsayin malami, ya taimaki rayuwar shugabannin gobe tare da gina cibiyoyin ilimi masu ƙarfi,” in ji Shugaba Tinubu.

Source: Twitter
Yayin da yake tunawa da lokacin mulkinsa a matsayin gwamnan tsohuwar jihar Oyo, Shugaba Tinubu ya ce:
“Duk da yake bai daɗe ba a kan mulki, an san shi a matsayin mai hangen nesa da kyakkyawan jagoranci. Kwace mulkin da sojoji suka yi bai hana shi ci gaba da hidima ga ƙasa ba.”
Shugaba Tinubu ya yi ta'azuyyar Olunloyo
Bola Tinubu ya yabawa marigayi Dr. Olunloyo bisa ƙaunarsa ga haɗin kan Najeriya da bunkasa ilimi, yana mai cewa gudunmawarsa za ta ci gaba da zama ginshiƙi a tarihin ƙasa.
“Allah Ya jikansa da rahama, Ya kuma ba iyalansa da duk masu jimami haƙurin jure wannan babban rashi,” in ji Tinubu.
Tsohon ɗan Majalisa a Oyo ya rasu
A baya, kun ji cewa tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Oyo, Kehinde Subair, ya riga mu gidan gaskiya ranar Juma'a.
Bayanai sun nuna cewa marigayi Kehinde Subair ya riƙe muƙamin ɗan Majalisar Dokokin Jihar Oyo har sau biyu a tarihin siyasarsa kafin Allah ya ɗauki rayuwarsa.
Sanatan Oyo ta Tsakiya, Yunus Akintunde ya bayyana mutuwar Subair a matsayin babban rashi ga jam’iyyar APC da ƙasa baki ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


