'Ana Kulla wa Ribas Makirci,' Kwamishinan Fubara Ya Hango Sabuwar Matsala
- Kwamishinan ci gaban matasa da aka dakatar a Ribas, Chisom Gbali, ya na zargin cewa akwai wata makarkashiya da ake shirya wa jihar
- Gbali ya ce sun ga alamun shirye-shiryen tsohon jami'in sojan ruwa, Ibok-Ete Ibas, wanda ya nada shugaba Bola Tinubu a matsayin mai kula da jihar
- Ya zargi tsohon gwamna, Nyesom Wike da mutanensa da kokarin tada zaune tsaye da tada hankali domin samun dalilin tsawaita dokar ta-baci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers - Kwamishinan ci gaban matasa da aka dakatar a Ribas, Chisom Gbali, ya bayyana cewa ana ci gaba da kitsa wani shiri na kara wa’adin dokar ta-baci da aka saka a jihar.
Gbali ya yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, tare da abokan tafiyarsa, na kitsa sabuwar tarzoma a domin a samu dalilin ci gaba da kakaba wa Ribas dokar ta-baci.

Asali: Facebook
A hira da ya yi da Arise News, Gbali ya bayyana sun ga alamun da tsohon jami'in sojan ruwan Najeriya Ibok-Ete Ibas ke nuna wa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya nada Ete Ibas a matsayin mai kula da jihar na tsawon watanni shida, bayan an dakatar da gwamna Siminalayi Fubara.
Ribas: Ana fargabar kara wa'adin dokar-ta-baci
Legit.ng ta ruwaito cewa yayin da ya ke bayyana ra’ayinsa kan lamarin a ranar Litinin, Gbali ya ce sun gano dukkanin motsin da wasu ke yi na kokarin tayar da husuma a Ribas.
A cewarsa:
“Wasu mutane a cikin jihar na kokarin tada zaune tsaye da tayar da hankali ga al’umma don hakan ya sa shugaban kasa Tinubu ya tsawaita dokar ta-baci.
"Halin da mai kula da jihar ke nuna wa da kuma matakan da yake dauka na nuni da cewa an tsara wannan shiri tun tuni.”
Kwamishinan gwamna Fubara ya caccaki Wike
Gbali ya ci gaba da zargin Nyesom Wike da mutanensa da cewa suna kokarin ganin shugaban kasa ya sake fitar da wata sanarwa domin tsawaita wa’adin dokar ta-baci a jihar.

Asali: Instagram
Ya ce:
“Idan aka samu karin wa’adi ko kadan ne, hakan na nufin gwamnatin Fubara ta zo karshe. Sun riga sun tsara yadda za su nada mutum guda a matsayin mai mulki a matakin kananan hukumomi.”
Ya kara da cewa:
“Tsohon gwamnan, wanda yanzu shi ne Ministan babban birnin tarayya Abuja, tare da abokan tafiyarsa, ciki har da ‘yan majalisar dokoki da shugabannin kananan hukumomi da wa’adinsu ya kare da gwamnatin jihar ta riga ta sanar da nadin rikon kwarya – su nake nufi. Mun san su, kuma ba za mu ci gaba da yin shiru ba.”
Mazauna Ribas sun tsunduma zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa wata sabuwar zanga-zanga ta barke a jihar Ribas, inda 'yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar da suka kasance a filin Isaac Boro da ke Fatakwal.

Kara karanta wannan
'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi
Masu zanga-zangar, wadanda suka fito da yawansu sun taru da safiyar ranar Litinin, misalin karfe 9:00 n.s, domin bayyana korafe-korafensu ga gwamnati da neman a dawo da gwamnansu.
Ana gudanar da zanga-zangar ne bayan an zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da tauye hakkin dan adam, tare da amfani da doka a kan intanet wajen tauye hakkin fadar albarkacin baki.
Asali: Legit.ng