Haduwar Izala: Sheikh Yusuf Sambo Ya Yi Kira ga Jingir da Bala Lau

Haduwar Izala: Sheikh Yusuf Sambo Ya Yi Kira ga Jingir da Bala Lau

  • Sheikh Yusuf Sambo ya roki malamai da dattawan Izala da su dawo su dunkule, yana mai cewa mutanen kirki sun mutu da damuwar rabuwar kungiyar
  • Malamin ya bayyana cewa haduwar kungiyar zai zamo alheri ga Musulunci, Najeriya da duk wani Musulmi a fadin kasar nan
  • A daya bangaren, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya marawa kiran baya, inda ya bukaci shugabannin Izala su zauna domin sulhu da hada kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Mataimakin shugaban malaman Izala, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya yi kira da a sake haduwar kungiyar da ke da bangarori biyu a yanzu.

Sheikh Yusuf Sambo ya ce ya samu kwarin gwiwa ne bayan Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ba Sheikh Abdullahi Bala Lau kariya kan zargin da aka masa.

Kara karanta wannan

'Ka da ka jawo mana rigimar addini': 'Yan sanda ga malamin Musulunci a Gombe

Yusuf Sambo
Sheikh Yusuf Sambo ya yi kira da sake haduwar Izala. Hoto: Saleem Yusuf Muhammad Sambo
Asali: Facebook

Legit ta gano cewa ya bayyana haka ne a wani bidiyo da Salem Yusuf Sambo ya wallafa a Facebook, inda ya ce lokaci ya yi da malamai za su dawo su dunkule waje daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Sambo ya ce malamai da dama da suka mutu kamar Sheikh Abubakar Gumi da Sheikh Abubakar Giro sun bar duniya cikin damuwa da yadda Izala ta rabu gida biyu.

“Rashin hadin kai na cutar da Izala” — Sheikh Sambo

Sheikh Yusuf Sambo ya ce lokaci ya yi da dattawan kungiyar Izala daga dukkan bangarori za su zauna wuri daya domin ceto da’awar Izala da kuma ci gaban dalibai.

Malamin ya ce:

“Idan aka hadu, an taimaki addini, an taimaki Najeriya, an taimaki dalibai. Idan da za mu gyara, za a daina yarfe wa juna,”

Malamin ya bukaci malamai da su hakura, su fahimci juna tare da saka hakuri a gaba idan suna fatan samun alheri da nasara.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da za a tuna Sheikh Idris Dutsen Tanshi da su bayan mutuwarsa

Sheikh Jalo Jalingo ya goyi bayan hadewar Izala

A nasa bangaren, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya bayyana goyon bayansa ga kiran Sheikh Yusuf Sambo na sulhu da hadin kai a tsakanin bangarorin Izala.

Ya ce ya saurari jawabin Sheikh Sambo a daren Lahadi 6 ga Afrilu, kuma yana ganin lokaci ya yi da shugabannin biyu za su zauna domin dinke baraka.

Sheikh Jalo ya ce ya kamata kowanne bangare ya rika gayyatar dayan bangaren a taruka na kasa, tare da ware wa wakilinsa lokaci don yin jawabi a hukumance.

Dr Jalo ya goyi bayan haduwar Izala
Dr Jalo ya goyi bayan haduwar Izala. Hoto: Ibrahim Jalo Jalingo
Asali: Depositphotos

Dr. Jalo ya yabi Sheikh Yusuf Sambo

Sheikh Jalo ya kara da cewa za a samu fahimta idan aka fara kyautata dangantaka da gayyatar juna a taruka.

Ya roki Allah ya hada zukatan bangarorin Izala da bunkasa da’awar bin sunnah a Najeriya da waje.

Dr Jalo Jalingo ya wallafa a Facebook cewa:

Kara karanta wannan

An kutsa gidan dan agajin Izala a Abuja, an sassara shi da makami har lahira

“Ina addu’ar Allah Ya saka wa Sheikh Yusuf Sambo da alheri bisa wannan kira da ya yi,”

Legit ta tattauna da Abdullahi Yakubu

Wani alaramma a bangaren Izalar Jos ya ce ba ya goyon a kara hada kungiyar matukar ba a magance matsalolin da suka haifar da rabuwa ba.

Abdullahi ya bayyanawa Legit cewa abin da ya fi dacewa shi ne a kyautata mu'amala da juna maimakon cewa za a hadu ba tare da an warware matsalolin ba.

"Kowa ya zauna a inda yake, a yadda yake. Amma a yi mutunci, a yi zaman lafiya, a yafewa juna a yi wa juna uzuri."

- Abdullahi Yakubu

Abubuwan da za a tuna Dutsen Tanshi da su

A wani rahoton, kun ji cewa a daren Juma'ar da ta gabata ne Allah ya yi wa Sheikh Dr Idris Abdul'azeez Dutsen Tanshi rasuwa.

Biyo bayan rasuwarsa, Legit ta hada rahoto na musamman kan abubuwan da za a tuna malamin da su.

Daga cikin abubuwan da Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya yi fice da su a lokacin rayuwarsa akwai fafatawa da shugaban Boko Haram, Muhammad Yusuf.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng