'Yan Bindiga Sun Kai Hari cikin Dare, Sun Hallaka Mutane a Katsina

'Yan Bindiga Sun Kai Hari cikin Dare, Sun Hallaka Mutane a Katsina

  • Wasu tsagerun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Ƴan bindigan sun kai harin ne cikin dare a wani ƙauye a Kankia, suka hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Miyagun sun kuma raunata wasu mutanen daban bayan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi lokacin da suka shiga ƙauyen
  • Jami'an tsaro sun kai agajin gaggawa bayan samun rahoton kai harin, amma kafin su isa ƴan bindigan sun tsere

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina.

Ƴan bindigan ɗauke da makamai sun kai harin ne a ranar 6 ga Afrilu, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare, a Unguwar Doruwa, wani ƙauye da ke kusa da Kunduru a cikin ƙaramar hukumar Kankia.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi tsaurin ido, sun farmaki sakataren gwamnatin Plataeu

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun hallaka mutum uku a Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Katsina

Bayanan sirri da aka samu daga wasu majiyoyi na tsaro sun bayyana cewa ƴan bindigan sun zo ne a kan babura, ɗauke da muggan makamai.

Ƴan bindigan sun yi amfani da duhun dare suka kutsa cikin ƙauyen, inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi tare da sace wasu shanu da suka tarar a cikin garin.

A yayin harin, sun kashe mutane uku nan take, sannan wasu mutum biyu suka samu munanan raunuka.

Bayan samun labarin harin, jami’an tsaro sun hanzarta kai ɗauki zuwa wajen da lamarin ya faru.

Sai dai kafin isowarsu, ƴan bindigan sun riga sun tsere daga yankin, wanda hakan ya sa ba a samu nasarar cafke su ba a lokacin.

Mutanen da suka jikkata a harin an garzaya da su zuwa asibitin koyarwa na tarayya da ke Katsina domin samun kulawar gaggawa daga likitoci.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun gwabza fada da 'yan Boko Haram, an samu asarar rayuka

An ce wasu daga cikin waɗanda aka harba sun samu raunuka masu muni, kuma suna samun kulawa ta musamman a asibiti.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina Hoto:@ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun kashe mutum uku

Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon wannan mummunan hari, yayin da ake ci gaba da lura da lafiyar waɗanda suka jikkata.

Wannan hari ya jefa jama’ar yankin cikin firgici da fargaba, inda da dama ke kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kara zage dantse wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Masu lura da sha’anin tsaro sun nuna cewa lamarin yana ƙara nuna bukatar inganta aikin leƙen asiri da kuma tabbatar da kai ɗauki cikin gaggawa idan ƴan bindiga sun kai hari.

Ƴan Lakuwa sun yi ɓarna a Kebbi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'addan Lakurawa sun hallaka jami'an tsaro na ƴan sa-kai a jihar Kebbi.

Ƴan ta'addan ɗauke da makamai sun hallaka ƴan sa-kai guda 13 a wani hari da suka kai a ƙaramar hukumar Augie ta jihar.

Lamarin ya auku ne bayan ƴan sa-kan sun yi wa ƴan Lakurawa kwanton ɓauna domin ƙwato shanun da suka sace.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel