'Farashin Litar Fetur zai Iya Sauka zuwa N350 a Najeriya,' Kungiyar Masu Matatun Mai

'Farashin Litar Fetur zai Iya Sauka zuwa N350 a Najeriya,' Kungiyar Masu Matatun Mai

  • Kungiyar masu matatun mai a Najeriya (CORAN) ta ce farashin man fetur na iya sauka kasa da N400 idan farashin danyen mai ya fadi zuwa Dala 50
  • CORAN ta ce duk da saukar da farashin danyen mai a kasuwar duniya, farashin zai ci gaba da hauhawa har sai an dawo da cikikin mai da Naira
  • Kungiyar ta dora alhakin hauhawar farashin fetur a kan farashin canjin dala, tsadar jigila, da kuma shiga tsakani da dillalai marasa jari ke yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar masu matatun man fetur (CORAN) ta ce akwai yiwuwar farashin man fetur ya sauka kasa da N400 idan aka ci gaba da amfani da danyen mai na cikin gida.

Kungiyar ta kara da cewa daidaita farashin dala zai iya kara sanya farashin man fetur ya karye warwas a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya za su siya fetur da araha bayan faduwar farashin gangar mai

Farashin mai
CORAN ta ce farashin mai zai iya sauka kasa da N400. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Punch ta wallafa cewa CORAN ta bayyana haka ne yayin da farashin danyen mai ya fadi zuwa $65, wanda hakan ke nuni da yiwuwar saukar farashin man da ake amfani da shi a cikin gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ganin cewa saukar farashi ya zo ne bayan karin hako man da kungiyar OPEC+ ta yi tare da kakkausar matsayar gwamnatin Amurka kan cinikin mai daga Venezuela.

'Man fetur zai iya dawowa N350' - CORAN

Jami’in hulda da jama’a na CORAN, Eche Idoko, ya ce idan aka kara karfafa aikin matatun cikin gida tare da faduwar farashin danyen mai zuwa Dala 50, babu dalilin da zai sa fetur ya fi N350.

Idoko ya ce:

“Na taba cewa idan aka bunkasa tace mai a cikin gida, za mu ga farashin man fetur yana sauka har zuwa N350.
"Kuma mun kusa cimma hakan kafin a dakatar da tsarin naira-da-danyen-mai.”

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 50, gwamna ya gano waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'adi

An zargi dillalai da dakile tace mai a gida

Idoko ya nuna damuwa da yadda wasu ‘yan kasuwa da dillalai ke kokarin hana nasarar tsarin tace mai a cikin gida domin su ci gaba da shigo da man gurbatacce daga waje.

Ya ce dillalan ba su zuba jari a harkar ba, amma su ne ke tsayar da farashi da kansu, suna amsar kudi babu wani dalili.

Yanayin farashin mai a halin yanzu

Duk da cewa farashin shigo da fetur ya fadi daga N885 zuwa N865 a makon da ya gabata, farashin da manyan diloli ke sayarwa ya karu daga N860 zuwa N900 a Lagos.

Idoko ya ce wannan yana faruwa ne saboda hauhawar farashin canjin Dala da kuma tsadar jigilar mai daga waje zuwa cikin Najeriya.

Gidan mai
Farashin danyen mai ya karye a kasuwar duniya. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

CORAN ta bukaci sayar da mai da Naira

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ci gaba da amfani da tsarin Naira domin sayar da danyen mai ga matatun cikin gida.

Kara karanta wannan

An yi albishir da saukar kudin sufuri da kayayyaki bayan karyewar farashin mai

Legit ta wallafa cewa CORAN ta ce yin hakan zai ba ‘yan Najeriya damar cin gajiyar arzikin man da Allah ya horewa kasar.

Alakar farashin sufuri da danyen mai

A wani rahoton, kun ji cewa an fara hasashen saukar farashin kayan masarufi bayan farashin danyen mai ya sauka.

Rahoton Legit ya nuna cewa masana sun ce za a iya samun saukin farashin kayan da ake aiki da su a yau da kullum bayan saukar farashin danyen mai.

Haka zalika ana hasashen cewa lamarin zai shafi farashin man fetur wanda zai kawo sauki kai tsaye a wajen sufuri ga 'yan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel