"Abin Tausayi": Mutane Sun Yi Magana, An Ji Yadda Aka Kashe Bayin Allah Sama da 50

"Abin Tausayi": Mutane Sun Yi Magana, An Ji Yadda Aka Kashe Bayin Allah Sama da 50

  • Mutanen karamar hukumar Bokkos a jihar Filato sun tsinci kansu cikin mummunan yanayi bayan hare-haren da aka kai masu
  • An ruwaito cewa akalla mutane 52 ne suka mutu a sabon rikicin da ya ɓarke yayin da wasu sama da 100 suka samu raunuka dabam-dabam
  • Waɗanda suka tsira daga waɗannan hare-hare sun bayyana azabar da ƴan bindiga suka gana wa mutanensu a Maris da farkon Afrilu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau - Mutanen da suka tsira daga hare-haren da aka kai a ranar 28 ga Maris da 2 ga Afrilu a Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato sun bayyana irin azabar da suka sha.

Waɗanda Allah ya tseratar daga hannun 'yan bindigar da suka afka musu ba tare da tsammani ba sun ce hare-haren sun yi muni sosai.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan abubuwa 4 da suka girgiza jama'a a makonni 2

Taswirar Filato.
Mutane sun ba da labarin azabar da suka sha a hare-haren ƴan bindiga a Filato Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Mutum nawa aka kashe a rikicin Filato?

Daily Trust ta tattaro cewa ƴan bindigar sun kai hare-haren ne a kauyuka da dama ciki har da Ruwi, Mangor, Daffo, Manguna, Hurti da Tadai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maharan sun kashe mutane da yawa, wasu suka jikkata, wasu kuma ba a san inda suke ba har kawo yanzu, cewar Vanguard.

Duk da cewa hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken rahoto ba tukuna, mazauna yankin sun ce akalla mutane 52 ne aka kashe, yayin da daruruwan wasu kuma suka samu raunuka.

Filato: Mutanen Bokkos sun ba da labari

A ranar Lahadi, wasu daga cikin wadanda suka tsira daga harin sun ba da labarin yadda lamarin ya faru. Tariza Jakob daga kauyen Hurti ta ce:

"Muna zaune lafiya ba tare da wata barazana ba, kwatsam ƴan bindiga suka shigo suka fara harbe-harbe. Muka fara gudu tare da yara, ba mu da inda za mu buya.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 50, gwamna ya gano waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'adi

"An kashe Mutane da dama, an ƙona mana gidajenmu. Muna rokon gwamnati ta taimake mu. Ba za mu taɓa yafe wa waɗanda suka kai mana wannan hari ba."

Michael Yuhana, wanda shi ma daga kauyen Hurti yake, ya ce:

"Lamarin ya faru da yammacin ranar Laraba. Ba zato ba tsammani muka fara jin harbe-harbe, kowa ya fara gudu. Duk da kokarin da muka yi na guduwa, sai da ak kashe gomman mutane.
"Lokacin da jami’an tsaro suka iso, an tabbatar da mutuwar mutum 35, yayin da 18 suka jikkata. Wasu har yanzu ba a gan su ba, an kai waɗanda suka jikkata asibiti. Jami'an tsaro sun yi ƙoƙari, amma ba su wadatar ba."

Abin da ya faru a garin Manguna

Banghas Atanguk daga kauyen Manguna ya ce:

"Misalin karfe 3:45 na rana muna cikin harkokinmu na yau da kullum sai muka fara jin harbe-harbe daga sassa daban-daban. Kowa ya fara gudu.

Kara karanta wannan

Bayan mummunan hari da Bello Turji ya kai, ƴan bindiga sun kona makaranta kurmus

"Wasu sun tsira, wasu ba su tsira ba, kawu na, Simon Bahias, shugaban makaranta yana cikin waɗanda aka kashe.
"Mu dai ga shi muna raye amma ba mu san me gobe ke ɗauke da shi ba. Jami'an tsaro suna ƙoƙari, amma ba su isa ba, sun yi kaɗan."

Sakataren gwamnatin Filato ya sha da ƙyar

A wani labarin, kun ji cewa sakataren gwamnatin jihar Filato, Mista Samuel Jatau, ya tsallake rijiya da baya da wasu ƴan ta'adda suka farmaki ayarinsa.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan ta'addan sun yi wa ayarin motocin kwanton ɓauna ne a ƙaramar hukumar Bokkos a ranar Lahadi, 6 ga watan Afirilun 2025.

An ce lamarin ya faru ne lokacin da sakataren gwamnatin ke hanyar zuwa ziyarar aiki a Bokkos, yankin da ƴan bindiga suka kai munanan hare-hare kwanaki baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel