Yadda Jihohi 20 Suka Rufe Ido, Sun Hana Ma'aikata Mafi Karancin Albashin N70,000

Yadda Jihohi 20 Suka Rufe Ido, Sun Hana Ma'aikata Mafi Karancin Albashin N70,000

  • Har yanzu, fiye da jihohi 20 a Najeriya ba su fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya ta aiwatar ba
  • Shugaban a NULGE na kasa, Haruna Kankara ya ce ma'aikatan kananan hukumomi da malaman firamare ba su fara morar kudin ba
  • Amma an samu wasu jihohi da suka fara aiwatar da tsarin sabon albashin, daga ciki har da Legas, Bayelsa, Enugu, Akwa Ibom da sauransu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Fiye da jihohi 20 a Najeriya har yanzu ba su fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 ga ma’aikatan kananan hukumomi da malamai na firamare ba.

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya (NULGE), Alhaji Haruna Kankara, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan abubuwa 4 da suka girgiza jama'a a makonni 2

Albashi
Ana zargin gwamnonin da kin biyan mafi karancin albashi Hoto: Dauda Lawal/Uba Sani/Abdullahi Bego
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa jihohin da suka hada da Yobe, Gombe, Zamfara, Kaduna, Imo, Ebonyi, Cross River, Babban Birnin Tarayya Abuja, Borno da wasu jihohi 11, ba su fara biyan sabon albashin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NULGE ta caccaki gwamnoni kan albashi

Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban NULGE ya koka cewa ma’aikatan kananan hukumomi da malamai na makarantar firamare a wadannan jihohi har yanzu ba su amfana da sabon albashi ba.

Bayan rattaba hannu a kan dokar sabon mafi karancin albashi na shekarar 2024, wasu jihohi suka fara aiwatar da sabon tsarin albashin.

Jihohin da ake biyan albashin akalla N70, 000

Jihohin da suka fara aiwatar da hakan sun hada da Legas, Ribas, Bayelsa, Neja, Enugu, Akwa Ibom, Abia, Adamawa da kuma Anambra.

Sauran jihohin da gwamnonin su ka farantawa ma'aikatan gwamnati rai su ne: Jigawa, Gombe, Ogun, Kebbi, Ondo, Kogi da sauransu.

Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya sa hannu kan dokar mafi karancin albashi na N70,000 a ranar 29 ga watan Yuli, 2024, bayan watanni ana muhawara tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 50, gwamna ya gano waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'adi

Yadda aka kara mafi karancin albashi

Sabon albashin na wata-wata ya karu da 133%, wato daga 30,000 zuwa N70,000, a daidai lokacin da ake fama da tsananin matsin tattalin arziki a fadin kasar.

A jawabinsa kan rashin aiwatar da sabon tsarin, Haruna Kankara ya ce:

“Gaskiya muna da matsala a wajen aiwatar da dokar a wasu jihohi da dama, kusan jihohi 20 ba su fara biyan sabon albashin ba.
Wasu daga cikinsu sun yi alkawari amma suka gaza cika alkawarin. Muna fatan nan ba da jimawa ba za a warware wannan matsala.”

A bangare guda, Kankara ya tabo batun aiwatar da cikakken ‘yancin kananan hukumomi, inda ya bayyana cewa Babban Bankin Najeriya bai fitar da wata sanarwa kan su bude asusu kai tsaye ba.

A cewarsa:

“Abin da ƙungiyarmu ke bukata tun farko shi ne CBN ya fitar da wata takarda ga kananan hukumomi don su bude asusun ajiya a bankin, amma har yanzu hakan bai faru ba.”

Kara karanta wannan

An fara gargadin gwamnatin Tinubu kan hana shigo da kayan sola Najeriya

Albashin jihohi ya karu a kasafin kudi

A baya, kun samu labarin yadda aka bayyana cewa jimillar kudin da jihohi 36 suka ware domin biyan albashi da alawus ya karu da 90%, inda ya kai N3.87trn a kasafin kudin shekarar 2025.

Wannan karin ya samu ne daga aiwatar da sabon tsarin mafi karancin albashi na N70,000 da kuma karin mukaman siyasa, kamar yadda alkaluman kasafin kudin jihohi suka nuna.

A watan Yuli 2024, Shugaba Tinubu ya amince da karin mafi karancin albashi zuwa N70,000, wanda ya sa gwamnonin suka bayyyana cewa sai an kara kasafin kudi don biyan ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel