'Yan Ta'adda Sun Yi Tsaurin Ido, Sun Farmaki Sakataren Gwamnatin Plateau

'Yan Ta'adda Sun Yi Tsaurin Ido, Sun Farmaki Sakataren Gwamnatin Plateau

  • Sakataren gwamnatin Plateau ya tsallake rijiya da baya a harin kwanton ɓauna da ƴan ta'adda suka kai wa ayarin motocinsa
  • Ƴan ta'addan sun kai farmaki ne kan ayarin motocin Samuel Nanchang Jatau a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Plateau
  • Harin na zuwa ne a lokacin da sakataren ke kan hanyar zuwa kai ziyarar aiki kan hare-haren da ƴan bindiga suka kai a Bokkos

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Ƴan ta'adda sun farmaki ayarin motocin sakataren gwamnatin jihar Plateau, Mista Samuel Jatau.

Ƴan ta'addan sun yi wa ayarin motocin kwanton ɓauna ne a ƙaramar hukumar Bokkos a ranar Lahadi, 6 ga watan Afirilun 2025.

'Yan ta'adda sun kai hari a Plateau
'Yan ta'adda sun farmaki sakataren gwamnatin Plateau
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Mista Samuel Jatau ya tsallake rijiya da baya a harin kwanton ɓaunan da ƴan ta'addan suka kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan ta'adda sun farmaki SSG a Plateau

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun gwabza fada da 'yan Boko Haram, an samu asarar rayuka

Ana kyautata zaton ƴan ta’addan suna shirye-shiryen kai sababbin hare-hare kan al’ummomin yankin, inda suka yi wa ayarin motocin kwanton ɓauna kusa da ƙauyen Hurti a gundumar Monguna.

Sakataren gwamnati jihar yana kan hanyar zuwa ziyarar aiki a Bokkos, inda ƴan bindiga suka kai munanan hare-hare a ranar Larabar da ta gabata.

Yayin da ayarin nasa ke cikin tafiya, ƴan ta’addan sun buɗe wuta a kan motocin, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka mayar da martani.

Saboda ƙarfin wutar jami’an tsaro, ƴan ta’addan sun janye suka shiga dajin da ke kusa da kuma tsaunukan da ke kewaye da wajen.

Sakataren gwamnatin Plateau ya yi Allah wadai

Bayan kwanton ɓaunar, SSG ya yi tir da harin, yana bayyana shi a matsayin rashin jin tsoron hukuma, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa kan matsalar tsaro a yankunan da abin ya shafa.

"Ba ni da kalmomin da zan bayyana baƙin cikina da fushi na. Mun ɗanɗana kaɗan daga cikin abin da mutanen nan ke fuskanta."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun samu gagarumar nasara

"Mun kusa faɗawa cikin kwanton ɓauna. Ina kallon wayata ne a cikin mota sai kawai na ji harbe-harbe. Da na ɗago kaina, sai na ga wasu matasa biyu ɗauke da bindiga suna guduwa cikin daji."

- Mista Samuel Jatau

'Yan ta'adda sun kai hari a Plateau
'Yan farmaki ayarin motocin sakataren gwamnatin Plateau Hoto: Fidex Nakwalla
Asali: Facebook

Yayin da yake bayyana irin ɓarnar da aka yi a yankin, Samuel Jatau ya ƙara da cewa:

"Mun ga irin ɓarnar da idonmu. Mutane fiye da 40 sun rasa rayukansu, gidaje sun lalace, dukiyoyi sun salwanta."
"Ƴan ta’addan sun wawashe kayayyaki masu muhimmanci kamar buhuna 26 na dankalin turawa daga gida guda, wanda kowanne ke da darajar Naira dubu 80."
"Waɗannan ƙananan manoma, ta yaya za su farfaɗo da rayuwarsu? Dole mu fi haka a matsayin ƙasa."

SSG ɗin ya kuma bayyana buƙatar ƙara tsaro a yankin, yana mai cewa hakan babban abin damuwa ne ga gwamnatin jihar.

Tinubu ya yi Allah wadai da hare-hare a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da hare-haren da ƴan bindiga suka kai a jihar Plateau.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kwanton bauna, sun hallaka 'yan kasar waje da dan sanda

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa irin waɗannan munanan ayyukan ta'addancin ba abu ba ne wanda za a amince da shi.

Ya umarci jami'an tsaro da su zaƙulo masu aikata laifin domin su fuskanci hukunci daga wajen hukuma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng