‘Ka da Ka Jawo Mana Rigimar Addini’: 'Yan Sanda ga Malamin Musulunci a Gombe

‘Ka da Ka Jawo Mana Rigimar Addini’: 'Yan Sanda ga Malamin Musulunci a Gombe

  • Rundunar ‘yan sandan Gombe ta nesanta kanta daga zargin wani malamin Musulunci, Sheikh Albany Gombe
  • ‘Yan sanda sun karyata zargi da kisan kai cewa wadanda ake zargin duk ba Musulmai ba ne
  • Rundunar ta gargadi jama’a su daina yada karya da kalaman da ka iya haddasa rikici

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Rundunar ‘yan sanda a jihar Gombe ta bayyana gaskiya kan bincike da take yi kan wani lamari da ya shafi fashi da makami da kisan kai.

Wannan bayani ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, wanda Sheikh Albany Gombe ya yi, yana zargin ‘yan sanda da rashin gaskiya.

Yan sanda sun kalubalanci malamin addini kan kalamansa
Yan sanda sun shawarci malamai su rika wa'azin zaman lafiya a cikin al'umma. Hoto: Buharee Abdullahi Dam Roni, Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe.
Asali: Facebook

Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce faifan bidiyon malamin cike yake da bayanan karya da kuma kalaman tada fitina ga jama’a, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kamar a Jahiliyya: An tono gawa bayan mahaifi ya kashe, ya birne 'yarsa a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin da Sheikh Albaniy ya yi

Malamin ya yi magana a cikin wani faifan bidiyo a Facebook inda ya ke kiran a dauki mataki kan matasan da suka yi kisan har da kwace babur.

Malamin ya ce dukan yaran da ake zargin wadanda aka kama babu Musulmi a ciki inda ya kalubalanci Gwamna Inuwa da kwamishinan 'yan sanda.

Ya ce ba za su taba yarda da cin zarafin al'umma ba saboda babu abin da ba su sani ba da ke faruwa saboda samun labaran tsaro.

Abin da rundunar ta ce kan zargin malamin

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa an kama Daniel Hamma mai shekara 36 da kuma Garba Usman wanda aka fi sani da Mali mai shekara 32 kan laifin fashi.

DSP Abdullahi ya ce an kai bincike gidan Garba Usman, inda aka gano babura guda biyu, gatari, sassan babura da kuma kayan ‘yan sanda.

Kara karanta wannan

'Ba mu san shi ba': 'Yan sanda sun kama 'ɗan sanda' da ya ce zai kashe 'yan Kudu a Arewa

Yace wadanda ake zargi sun amsa cewa sun aikata fashi da kisan kai a ranar 1 ga Maris, 2025, inda suka kashe wani mutum.

Bincike ya kai ga kama Bala Danyaya mai shekara 29 wanda ya amsa karbar babura guda shida daga hannun barayin daga 2024 zuwa 2025.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa zargin malamin cewa duk wadanda ake zargi ba Musulmai ba ne karya ne maras tushe.

DSP Abdullahi ya bayyana cewa Garba Usman da Bala Danyaya Musulmai ne, kuma irin wadannan kalaman na iya haddasa rikici a cikin al’umma.

Rundunar ta ja kunnen jama’a musamman wadanda ke da tasiri, da su guji yada bayanai marasa tushe ko tada hankali ga jama’a.

DSP Abdullahi ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.

Yara 2 sun mutu a filin idin Gombe

Mun ba ku labarin cewa Rundunar ‘yan sandan Gombe ta tabbatar da mutuwar yara biyu sakamakon turmutsutsu da ya auku a babban filin Sallar idi na Gombe a ranar sallah.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi halin da yake ciki bayan cewa ya yanki jiki ya fadi, an tafi da shi Faransa

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:45 na safe yayin da jama’a suka yi kokarin fita cikin gaggawa, lamarin da ya janyo jikkatar mutum 22.

Tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata asibitoci daban-daban, yayin da Gwamna Inuwa Yahaya ya dauki nauyin jinyar dukkan wadanda suka sami raunuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel