Adamawa: Ɗan Atiku Ya Kare Kansa da Aka Masa Rubdugu kan Ziyarar da Ya Kai Gidan Sarki
- Ɗan tsohon mataimakin shugaban kasa, Aliyu Atiku Abubakar ya kare kansa kan ziyarar da ya kai wa sarkin Fufore, Muhammad Sani Ribaɗu
- Aliyu ya bayyana cewa sabon sarkin Baffan matarsa ne kuma ya kai masa ziyara ne a matsayin suruko ba wai yana goyon bayan ƙirƙiro masarautu ba ne
- Ɗan Atiku ya yi wannan bayani yayin da magoya bayan mahaifinsa suka fara sukar ziyarar da ya kai wa basaraken
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa - Aliyu Atiku Abubakar (Turakin Adamawa) kuma ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi bayani kan ziyarar da ya kai masarautar Fufore.
Aliyu ya musanta zargin cewa ziyara da ya kai wa Sarkin Fufore, Muhammad Sani Ribadu, na da nasaba da goyon bayan sababbin masarautun da aka ƙirƙiro a Adamawa.

Kara karanta wannan
'A tsaye aka karɓi ta'aziyya ta': Sheikh ya fadi dattakun ɗaliban Malam Dutsen Tanshi

Asali: Facebook
Ɗan Atiku ya yi wannan bayani ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Asabar, 5 ga watan Afrilu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masoyan Atiku sun soki ziyarar Aliyu
Ziyarar da ɗan tsohon mataimakin shugaban kasar ya kai masarautar Fufore ta tayar da ƙura a siyasar jihar Adanawa musamman daga masoyan Atiku Abubakar.
Galibin magoya bayan Atiku sun yi zargin ziyarar na da nasaba da goyon bayan sababbin masarautun da Gwamna Ahmadu Fintiri ya kirkiro domin rage tasirin Lamidon Adamawa.
Wannan ziyara da Aliyu Atiku Abubakar ya kai ga sarkin Fufore, ɗaya daga cikin sababbin sarakunan Adamawa kuma ɗan'uwan Nuhu Ribadu ta tayar da ƙura.
Sarkin Fufore ɗan uwa ne ga mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribaɗu kuma Aliyu yana auren ɗiyar NSA.
Ɗan Atiki ya fito ya kare kanta
Da yake martani kan batun, Aliyu Atiku, Turaki Adamawa ya ce:
"Ya kamata ku sani sabon sarkin Baffan matata ne. Matata tana tsayawa tare da ni da dangina a kowane lokaci, cikin farin ciki ko bakin ciki. Ina matuƙar jin daɗin wannan goyon baya daga gareta.
"Kuma ina ganin ya dace nima na nuna girmamawa da kyautata hulɗa da dangin matata ma'ana surukaina, ya kamata mutane su sani kowane yana da rayuwarsa baya ga siyasa."
Aliyu ya ƙara da cewa ya kamata a raba siyasa da al’amuran rayuwa ta yau da kullum, inda ya ƙara da cewa:
"Akwai rayuwa bayan siyasa, ba komai ake alaƙanta shi da siyasa ba, ina ƙara godewa iyaye na da suka tarbiyyantar da mu yadda za mu banbance su.

Asali: Facebook
Shin ɗan Atiku ya koma bayan Gwamna Fintiri?
Game da zargin cewa ziyarar na nufin goyon bayan Gwamna Fintiri sabanin ra’ayin mahaifinsa, Aliyu ya bayyana matsayinsa cikin girmamawa da biyayya ga Lamidon Adamawa:
"Biyayyata ga mai martaba Lamido Barkindo Aliyu Mustapha ta na nan daram. Na ji daɗi da girmamawa matuƙa lokacin da ya naɗa ni Turakin Adamawa ina da shekaru 25, hakan na ɗaya daga cikin karramawar da na samu a rayuwata."

Kara karanta wannan
An bar kasa ba kowa: Shettima ya shilla kasar waje bayan Tinubu ya kwana a Faransa
"Idan wani na tunanin zai iya tayar da rigima a cikin dangina ta hanyar siyasantar da rayuwarmu, to ya sani ya kama hanyar da ba za ta ɓulle ba."
An maka gwamnatin Adamawa a kotu
A wani labarin, kun ji cewa wasu mutum uku a masarautar Adamawa sun kai karar gwamnatin Ahmadu Finrtiri kan kirkiro sababbin masarautu.
Babbar kotun ta jihar Adamawa ta fara sauraron ƙarar wacce Musa Halilu Ahmed, Alhaji Mustapha Dahiru Mustapha, da Alhaji Mustapha Ahmad, suka shigar gabanta.
Masu karar na ikirarin cewa kafa masarautar Fufore yana barazana ga tarihi da al’adar masarautar Adamawa, wadda ta dade a tarihin jihar.
Asali: Legit.ng